Kasar Sin Za Ta Zuba Jari A Karamar Hukumar Birnin Kudu
Published: 31st, January 2025 GMT
Karamar Hukumar Birnin kudu ta jihar Jigawa ta bada tabbacin hada kai da duk wata hukuma ko kamfani dake da muradin cigaban yankin.
Shugaban karamar hukumar, Dr. Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin lokacin da wakilan rukunin kamfanonin kasar Sin wato China suka ziyarce shi a ofishinsa.
Yace karamar hukumar Birnin kudu tana sahun gaba wajen zaman lafiya da karbar baki a fadin jihar.
Mista Sheng ya shaidawa shugaban karamar hukumar niyyar sa ta kafa kamfanin sarrafa takin zamani a yankin domin bunkasa aikin gona.
Yana mai cewar zai samar da kamfanin yin kujeru da gado da sauran kayayyaki domin bunkasa al’amuran kasuwanci a yankin.
Yace zai kuma samar da sinadarin da zai taimakawa manoma wajen samun amfanin gona mai yawa a lokutan noman rani har ma da na damina.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, a fanin lafiya kuwa, a zancen da ake yi yanzu, hukumar kula da lafiya matakin farko ta karamar hukumar Birnin kudu da hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya sun yabawa shugaban karamar hukumar bisa kokarinsa na tallafawa al’amuran rigakafi a yankin.
Manajan hukumar Alhaji Bello Abdulkarim wanda ya jagoranci tawagar hukumomin biyu zuwa ofishin shugaban karamar hukumar, ya danganta nasarorin da ake samu bisa hadin kai da goyon bayan shugaban wajen gudanar da ayyukan rigakafi a yankin.
Da yake mai da jawabi, shugaban karamar hukumar Alhaji Muhammad Uba Builder, ya bada tabbacin ci gaba da tallafawa harkokin kiwon lafiya bisa la’akkari da muhimmacin ta.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Kasar Sin Zuba Jari shugaban karamar hukumar karamar hukumar Birnin
এছাড়াও পড়ুন:
Lavrov Ya Yi Watsi Da Batun Aike Wa Da Dakarun Zaman Lafiya A Kasar Ukiraniya
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai.
Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a ci gaba da yaki.
Sergey Lavro ya kuma ce; tunanin aikewa da dakarun zaman lafiya zuwa Ukiraniya wauta ce.
Lavrov ya bayyana shugaban kasar Ukiraniya Zelenskiyda cewa dan Nazi ne, wanda ya ha’inci al’ummarsa.”