An Samu Ci Gaba A Bangaren Kayayyakin Da Sin Ta Fitar Zuwa Kasashe Da Yankuna 160 A 2024
Published: 31st, January 2025 GMT
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024.
Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan 25.45, kimanin dala triliyan 3.
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Harbo Jirgin Leken Asirin Amurka Samfurin MQ9
Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib.
Janar Sari ya ci gaba da cewa za mu ci gaba da abinda muke yi na hana jiragen ruwa wuce ta tekun “Red Sea” domin zuwa HKI, tare da kara da cewa, ba kuma za mu yi taraddudin daukar dukkanin matakan kare kai ba, akan jiragen ruwan abokan gaba a nan gaba.
Kwanaki biyu da su ka gabata, sojojin Yemen sun kai wasu hare-hare akan jirgin dakon jiragen yaki na “Trauman’ da sauran jiragen yakin da suke ba shi kariya.
Sojojin na Yemen suna kuma ci gaba da kai wa HKI hare-hare da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami a karkashin taya Falasdinawa fada, da kuma yin kira da a kawo karshen takunkumin da aka kakaba musu.