NAJERIYA A YAU: Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa?
Published: 31st, January 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya?
Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna.
Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Demokradiyyar Kwango Ta Haramta Jam’iyyar Josept Kabila A Kasar Saboda Hulda Da Yan Tawaye
Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar.
Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan.
Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s Party for Reconstruction and Democracy (PPRD).
Daga baya Kabila ya dorawa kansa gudun hijira zuwa kasashen waje a shekara ta 2023. Bai kuma sake dawowa ba sai ranar jummar da ta gabata.
Kabila dan shekara 53 a duniya, ya shigo kasar kongo daga kasar Rwanda, sannan ya je ya gana da shuwagabannin kungiyar M23 a birnin Goma, inda daga nan suke ikonsu a kan yankunan arewa da kudancin Kivu.
Gwamnatin tsetsekedi tana zargin Kabila da goyon bayan yan tawayen M23, haka ma ta bayyana cewa Jami’an tsaron kasar sun kai farmaki a kan gidan Kabila da ke kinsasa da wata gonarsa, iyalan Josepy Kabilan sun tabbatar da haka.
Makonni kafin dawowarsa gida, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa zai dawo kasarsa ne don ya taimaka wajen dawo da lafiya cikin kasar.
Daga karshe a wani bangare kuma ma’aikatar sharia ta kasar ta bayyana cewa ta fara shirin gabatar da Kabila a gaban kuliya saboda goyon bayan kungiyar M23.