Kungiyar Hamas Ta Lashi Takwabin ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa
Published: 31st, January 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan mamayar Isra’ila
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan sahayoniyya, tare da yin nuni da cewa, za ta ci gaba da kokarinta ba tare da wata matsala ba, domin kubutar da su ta kowace hanya.
Kungiyar Hamas ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a a yayin bikin sakin wani sabon rukunin fursunonin Falasdinu, tana jaddada cewa: Hamas ta sake sanar da babban alfahari da girmamawa ga al’ummar Falastinu masu tsayin daka, a daidai lokacin da aka sako wani sabon rukunin fursunonin Falasdinawa wadanda suke jarumai daga gidajen yarin yahudawan sahayoniyya, bayan gwagwarmaya ta tilasta musu bude kofofin gidajen yarinsu domin sake Falasdinawa, kuma karkashin yarjejeniyar dakatar da wuce gona da iri da musayar fursunoni.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: fursunonin Falasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama’a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama’a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da jami’an hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin kidayar jama’a ga tsare-tsare na kasa, tare da jaddada aniyarsa na tabbatar da tattara bayanai masu inganci.
Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa kwamitin da zai duba kasafin kidayar jama’a da kuma gano hanyoyin samun kudade.
Ya kuma jaddada bukatar hukumar kula da tantance ‘yan kasa (NIMC) ta taka rawar gani wajen gudanar da wannan aiki, tare da tabbatar da samar da ingantattun na’urorin tantancewa da suka hada da tantance fuska da murya.
Shugaban ya bayyana cewa ingantattun bayanan za su haɓaka shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannin aikin gona da walwalar jama’a.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya tabbatar da kudurin na Tinubu, inda ya bayyana cewa rashin kudi ne ya janyo tsaikon kidayar jama’a.
Ya kuma bayyana cewa, NPC ta riga ta kammala muhimman ayyukan shirye-shirye da suka hada da kidayar jama’a, sannan kuma hukumomin tantancewa da kididdiga daban-daban kamar su NPC, NIMC, NBS, da Ma’aikatar Tattalin Arziki, suna aiki tare don inganta bayanan da ake da su.
Daga Bello Wakili