Leadership News Hausa:
2025-04-22@18:20:55 GMT
Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha
Published: 31st, January 2025 GMT
Dakta Tingilin ya ce a cikin wannan shekarar, gwamnatin Jihar Katsina ta yi kasafin kudi na naira miliyan dubu 50 domin tabbatar da samar da tsabtataccen ruwan sha a kananan hukumomi 20 na cikin jihar.
Ya kara da cewa kwamitin karbar korafe-korafe da aka kafa, an kafa shi ne domin duba aikace-aikacen shirin SURWASH da ake gudanarwa ga al’ummar a jihar.
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar, sakamakon yawaitar hare-hare da kashe-kashen da ake yi a birnin. A cewar gwamnan, an takaita zirga-zirgar babura da masu tuka keke napep a tsakanin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe. Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati, ranar Talata. Ya ce, amma dokar ta kebe cibiyoyi da hukumomin kiwon lafiya. Ya bayyana cewa, sabon matakin na da nufin dakile matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa a babban birnin jihar. Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnati ba za ta rungume hannu ba, yayin da masu aikata laifuka ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Ya kuma umurci gundumomi, ƙauye, da masu unguwanni da su sanya ido kan duk wadanda ke zaune a yankunan su. Ya kuma yi gargadin cewa, duk gidan da aka samu yana dauke da masu aikata laifuka ko masu safarar miyagun kwayoyi za a ruguza shi. A baya-bayan nan dai garin Minna ya sake samun koma-baya na ‘yan daba, da hare-hare, da kashe-kashe, lamarin da ke janyo firgici da damuwa a tsakanin mazauna garin.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp