Leadership News Hausa:
2025-04-23@01:14:57 GMT

Kadan Daga Hakuri Da Yafiya Da Rangwamen Annabi (SAW)

Published: 31st, January 2025 GMT

Kadan Daga Hakuri Da Yafiya Da Rangwamen Annabi (SAW)

Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba.

Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba.

Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba.

Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa “kuzil afwa, wa’amur bil ma’rufi, wa a’arid anil jahilin” ya rasulallahi ka yi rangwame, ka yi umurni da abin da shari’a ta saukar maka sannan kuma ka kauda kai ga jahilai masu yi maka wauta. An ruwaito daga Annabi (SAW) yayin da aka saukar masa da wannan ayar, ya ce ya Jibrilu mece ce fassarar wannan ayar, sai Jibrilu ya ce ni ma sai na tambayi masani (Allah), sai Jibrilu ya tafi tambaya (inda yake ganawa da Ubangiji) bayan ya dawo sai ya ce ya rasulallahi, “Ubangijinka yana horon ka da ka sadar da zumunci ga wanda ya yanke maka, ka ba wa wanda ya hana ka, ka yi rangwame ga wanda ya zalunce ka” wadannan su ne manyan dabi’u duk da cewa, akwai wasu hadisai da suke bayyana cewa, mutum ya yi zamansa a wuri daya ya fi, hadisin yana cewa “Gidanka ya isar maka (in ka san wanda ya yanke maka, zuwanka gare shi zai saukar da wutar bala’in da ke zuciyarshi, wannan zuwan ya fi zama a gida, amma in zuwanka wurinshi bala’in ne zai karu, zamanka ya fi zuwa) wanda ya hana ka, ka ba shi – in wani bala’in ba zai kara kunno kai ba, ka yafe wa wanda ya zalunce ka.”

Ubangiji ya kara cewa Annabinsa (SAW) “wasbir ala ma’asabak, inna zalika min azmil umur,” ma’ana ka yi hakuri kan abin da ya same ka, lallai hakuri kan bala’i yana daga cikin manyan abubuwa. “fasbir kama sabara ulul azmi minarrusul…” ka yi hakuri kamar yadda manya daga cikin Annabawa suka yi “wal ya’afu wal yasfahu…” ku yi afwa ku yi rangwame “ala tuhibbun an yagfirallahu lakum wallahu gafurun Rahim” shin ba ku son ku ma Allah ya yi muku gafara ne, Allah mai gafara ne kuma mai jin kai.

Imam Turmizi ya ruwaito hadisi daga Urwatu shi kuma daga uwar Muminai Sayyada A’isha ta ce, ba a taba kawo wa Annabi (SAW) zabin abu biyu ba face sai ya zabi mafi sauki, matukar mafi saukin bai zama zunubi ba, Annabi (SAW) bai taba fushi ba don wani ya taba shi sai dai in wani aka taba ko kuma akwai hakkin Allah a ciki. “Duk wanda ya jibinci lamarin Allah, shi ma Allah zai jibinci lamarinshi”

An ruwaito cewa yayin da aka karya hakorin Manzon Allah (SAW) a ranar yakin Uhudu, hakorin ya yi tsanani a gareshi, sai sahabbai suka ce “Ya rasulallahi, da ka yi musu bakar Addu’a” Sai ya ce musu, ba a aiko ni in tsine wa mutane ba sai dai in zama Rahma a gare su. Allah Ka shiryar da Mutanena, ba su sanni ba ne.

An ruwaito daga Sayyadina Umar RA ya ce: Na ba da fansar Iyayena a gare ka, Annabi Nuhu ya yi wa Mutanensa bakar addu’a da cewa “Allah kar ka bar ko digon kafiri daya a kan kasa, duk ka hallakar da su”. Ya Rasulallahi da ka yi irin wannan adu’ar a kanmu kafin Musulunta, da tuni mun halaka dukkanmu, an cutar da kai, an zubar maka da jini, an karya hakorinka amma duk da haka sai ka fadi alkhairi a kanmu ba ka yi mana muguwar addu’a ba. Amma rahama da tausayi da rangwame na Annabi (SAW), bayan ya yafe musu kuma sannan ya nema musu afuwa da kafa musu hanzarin cewa “Ya Ubangiji ba su sanni ba ne.”

Yayin da wani ya jefi Manzon Allah (SAW) da cewa, ya rasulallahi “ka yi adalci” a yakin Hunaini sai (SAW) ya ce “kaiconka! wa ye zai yi adalci in ban yi adalci ba, ashe na tabe” ya hana wanda ya yi nufin ya sare masa kai na daga Sahabbansa da fadinsa ya za kai da zuriyar da zai bari bayansa.

Wannan mutumi shi ne ake kira Zulkhuwaisarah, Mutum ne mai yawan Sallah da karatun Alkur’ani, sabida yawan Azumi duk idanuwansa sun faffada amma babu girman Annabi (SAW) a zuciyarsa. A ranar yakin Sayyadina Ali da tawagar khawarijawa aka kashe shi, Sayyadina Ali ya ce Annabi (SAW) ya fada masa a wannan yakin za a kashe shi, Sayyadina Ali ya ce a binciko gawarshi sabida Annabi (SAW) ba ya karya, an shafe tsawon lokaci ana neman gawarshi amma ba a gani ba, bayan duba gawarwakin da suka fada cikin wani Rami, sai gashi an zakulo gawarshi. Annabi (SAW) ya yi gaskiya.

Akwai wani Kafiri da ake kira Gaurasu bin Harisu, ya taba bijiro wa Annabi (SAW) da nufin kashe shi yayin da Annabi (SAW) shi kuma ya koma gefe daya jikin wata bishiya yana hutawa ya rataye takobinsa jikin bishiyar, sai Gaurasu ya lallabo ya dauki takobin ya ce wa Annabi (SAW) “Yau waye zai kare ka” take Annabi (SAW) Ya ce masa ‘Allah’ kawai sai takobin ta fadi, Annabi (SAW) ya dauki takobinshi ya ce wa Kafiri Gaurasu, “kai kuma waye zai kare ka yau?” sai ya ba da amsa cewa, ka zama fiyayyen wanda ya dauki takobi ko kuma abin da ka fada ya kare ka, ni ma shi zai kare ni, in ji Gaurasu. Sai manzon Allah (SAW) ya yafe masa, ya koma wurin mutanensa ya ce musu, na zo wurinku daga wurin mafificin mutane.

Yana daga cikin labarun Annabi (SAW) kan yafiya, yafewarsa ga Bayahudiyar nan da ta sa masa Guba cikin naman akuya, da aka kama ta ta ce, tana sane ta sa gubar da nufin cewa; In Annabi (SAW) sarki ne kawai, ya mutu a huta, in kuma da gaske Annabin Allah ne, Ubangijinsa zai kiyaye shi. A wata ruwaya, Annabi Ya sa a kashe ta sabida akwai wani sahabi da ya ci kuma ya rasu nan take. Ingatattar ruwaya ita ce, Annabi (SAW) ya yafe mata amma sabida mutuwar wani daga cikin Sahabbansa bayan cin gubar, Annabi (SAW) ya sa a kashe ta.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: ya rasulallahi Ya rasulallahi

এছাড়াও পড়ুন:

Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu

A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci.

Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama.

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza.

Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba.

A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa kan kamun da aka yi wa wadda yake karewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Zata Gudanar Da Tarin Kare Hakkin Bil’adama Ta Faskar Gabacin Duniya A Karo Na Farko
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 112
  • Fafaroma Francis ya Rasu
  • Yadda ma’aikatan gidan ruwa 4 suka mutu a Bauchi
  • Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
  • Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
  • Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja
  • Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari?
  • Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu