Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Tirela Ta Kwace A Legas
Published: 31st, January 2025 GMT
Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin sansanin Sojojin.
Sojan (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a cikin motar akwai matasa uku da ake zargin ‘yan damfara ne, masu amfani da intanet (Yahoo Boys). Bayan hatsarin, ɗaya daga cikinsu ya tsere, yayin da sauran biyun aka kama su, aka yi musu dukan tsiya, tare da lalata motarsu.
Zamu kawo cikakken labarin nan gaba…
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo.
A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — NatashaKazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa da kuma kwantar da hankalin al’ummar Kano.
Haka kuma, shugaban ƙungiyar Nworisa Micheal, ya yi watsi da zancen da ke yawo a soshiyal midiya cewa wasu matasa sun halaka wani dan ƙabilar Ibo ibo mai suna Peter Chukwudi Nwanosike, ɗan asalin garin Abagana da ke Anambra mazauni a Kano, a matsayin martani kan kisan mafarautan.
“Saɓanin abin da ake yaɗawa ba kashe shi aka yi ba, tsautsayin masu ƙwacen waya ne ya afka kuma ya yi ƙoƙarin tserewa. Babu wanda ya caka masa makami kamar yadda ake yaɗawa.”
Ƙungiyoyin sun kuma gargaɗi kafafen yaɗa labari kan illar watsa labarai ba tare da bincike ba.
Kazalika sun yaba wa Sarkin Edo kuma Enogie II, Fred Edozele Akhigbe (JP), kan fitar da sanarwar yin tir da lamarin da ya faru a Edon sa’o’i kaɗan bayan faruwarsa, da gwamnan jihar, Monday Okpebholo, kan ziyarar jajen da ya kawo Kano, da kuma ƙoƙarinsa na samar da haɗin kai da adalci kan waɗanda lamarin ya rutsa da su.