A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024.

Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci.

Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC.

Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban 2024, kason hauhawar farashin kayan masarufi ya kai zuwa kaso 34.8 lamarin da ke kara lafta wa ‘yan Nijeriya damuwuwi musamman na yadda suke kasa iya sayen ababen bukata kama daga kayan abinci, gidaje da kuma kiwon lafiya.

Daga watan Janairu zuwa Satumban 2024, sufuri da kayan abinci su ne aka samu karuwa sosai a kansu. Tashin kudin man fetur shi ne ya janyo dukkanin tashin kudin sufuri da na kayan abinci.

Karuwar farashin kayan abinci na nuni da barazanar adana abinci da ake ciki, wanda ya shafi ‘yan Nijeriya miliyan 25.1 a 2024. Sai dai rahoton na PwP ya yi gargadin cewa adadin zai iya karuwa zuwa miliyan 33.1 a 2025 muddin hauhawar farashin ya ci gaba da tashi.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta biyo da wasu tsare-tsaren da take ganin za su saukaka kamar karancin albashi, sai dai kaso 4.1 cikin 100 kacal na ‘yan kasar ne ke aiki, lamarin da ke nuni da cewa hakan ba zai yi tasiri ba.

Masu ruwa da tsaki sun lura da cewa lamarin karuwar masu fadawa cikin talauci lamari ne da ke bukatar daukan matakan gaggawa na shawo kan matsalolin da suka dabaibaye tattalin arziki. Duk da karuwar tattalin arzikin Nijeriya na GDP da kaso 3.0 a 2024 akwai bukatar kara himma a 2025.

Rahoton ya yi kira da a samar da ingantattun matakan kawar da fatara, gami da sa kaimi ga al’umma da gyare-gyaren tsari don magance hauhawar farashin kayayyaki da bunkasar tattalin arziki mai dorewa.

A cewar rahoton, idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba, matsalar tattalin arzikin da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fuskanta zai kara tabarbarewa tare da jefa dimbin iyalai cikin fatara da kuma kawo cikas ga ci gaban kasar na dogon lokaci.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tattalin arzikin yan Nijeriya kayan abinci

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

 

Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.

 

A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da tsaron lafiyar jama’a.

 

Don haka rundunar ta bukaci mazauna kauyen Tsohon Kafi da kewaye da kada su firgita da jin karar harbe-harbe a yayin atisayen.

 

Abdullahi ya ce, za a sanya ido sosai a kan dukkan ayyukan da kuma gudanar da su a cikin yanayi mai aminci da kulawa.

 

Rundunar ta kuma yaba da ci gaba da goyon baya da hadin kan al’umma wajen tallafawa kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

 

KARSHE/USMAN MZ

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
  • Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa
  • Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayi
  • Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu
  • Minista Ya Sake Jaddada Ƙudirin Sabunta Kayan Aikin Watsa Labarai Na Gwamnati
  • Duk Da Matsin Rayuwa: Bankuna Na Ci Gaba Da Cin Kazamar Riba Ta Hanyar Dora Wa Al’umma Haraji
  • ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista
  • Alkaluman Tattalin Arzikin Sin Sun Shaida Dorewar Ingancin Tattalin Arzikinta
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100
  • Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba