Aminiya:
2025-04-02@17:43:21 GMT

Isra’ila ta kashe Palasdinawa 10 ta kama 12 bayan musayar fursunoni 110

Published: 31st, January 2025 GMT

Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu.

Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas.

Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan.

Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan uwansu 110 da Isra’ila ta yi daga gidajen yarinta a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya a Zirin Gazan.

An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zina Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’a

Jami’an tsaro na Isra’ila na ci gaba da kai hare hare da tsare Palasdinawa ne duk yarjejeniyar zaman lafiyar da ake aiwatarwa a Zirin Gazan.

Kawo yanzu Palasdinawa 47,460 ne aka kashe, tare da jikkata wasu  111,580 tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023 da aka fara wannan yaki.

An kashe wasu kimanin 1,139 a Isra’ila a lokacin da kungiyar Palasdinawa ta Hamas ta kai hai a ranar, inda ta yi garkuwa da wasu kimanin 200, ciki har da baki ’yan kasashen waje.

‘Yan sandan Isra’ila sun kama wasa Palasdinawa 12 da ke murnar sako ’yan uwansu 110 daga gidajen yarin Isra’ila a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya a Zirin Gazan.

Jami’an tsaron Isra’ilar sun tsare mutanen ne a yankin Gabashin Birnin Kudus saboda suka murnar sako Palasdinawa da Isra’ila ta tsare a gidajen yarinta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila Palasdinawa

এছাড়াও পড়ুন:

DG VON Yayi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Don Fadada Ci gaban Tattalin Arziki Da Ci Gaba.

Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata.

 

Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a Minna jihar Neja.

 

Malam Jibrin Baba Ndace ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ya zama wajibi saboda nasarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu ya kasance nasarar mu baki daya, don haka akwai bukatar mu kasance cikin nasara.

 

Daga nan sai ya mika gaisuwar ban girma ga daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya na bikin sallah karama tare da shawartar su da su dage wajen tallafa wa aikin Nijeriya domin samun sakamako mai ma’ana.

 

A cewarsa a madadin daukacin mahukunta da ma’aikatan gidan rediyon Muryar Najeriya, ina mika sakon gaisuwa da jinjina ga daukacin al’ummar musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya a daidai lokacin da muke gudanar da bukukuwan karamar Sallah mai albarka tare da shawartar su da su aiwatar da abin da suka koya a cikin azumin watan Ramadan.

 

Malam Jibrin Baba Ndace ya yi addu’ar Allah ya karawa ‘yan Najeriya farin ciki da walwala, da kuma sabon karfi domin su ci gaba da hada kai wajen samar da fahimtar juna, wajen bayar da gudunmawa mai kyau ga ci gaba da zaman lafiyar Nijeriya.

 

PR ALIYU LAWAL

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga, Sun Ceto Ɗalibai 2 A Nasarawa
  • Ma’aikatan Kasar Sin Sun Ceto Mutum 8 Zuwa Yanzu A Myanmar
  • Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF
  • Sin Da Zambiya Sun Daddale Yarjejeniyar Fitar Da Kwarurun Macadamia Nuts
  • DG VON Yayi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Don Fadada Ci gaban Tattalin Arziki Da Ci Gaba.
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
  • Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
  • Gwamna Umar Namadi Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Sallah Karama
  • Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
  • Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya