Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Tirela Ta Kwace A Legas
Published: 31st, January 2025 GMT
Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin sansanin Sojojin.
Sojan (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a cikin motar akwai matasa uku da ake zargin ‘yan damfara ne, masu amfani da intanet (Yahoo Boys). Bayan hatsarin, ɗaya daga cikinsu ya tsere, yayin da sauran biyun aka kama su, aka yi musu dukan tsiya, tare da lalata motarsu.
Zamu kawo cikakken labarin nan gaba…
এছাড়াও পড়ুন:
Yeman : Sojojin Amurka sun kai wani gagarumin farmaki kan lardunan Sanaa da Hudaidah
Mutane da dama ne suka mutu sannan wasu sun jikkata sakamakon wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Amurka suka kai kan wasu yankuna na kasar Yemen.
A daren jiya wayewar yau Lahadi, sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama akalla 20 a Sanaa babban birnin kasar Yemen, da kuma yammacinta da gabashi da kuma kudancin kasar.
Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar Yemen suka sanar a ranar Asabar cewa kimanin mutane 80 ne suka mutu, yayin da wasu 150 suka samu raunuka sakamakon harin da Amurka ta kai a ranar Juma’a a tashar mai na Ras Issa da ke birnin Hudaidah.
Hare-haren na Amurka a Yemen sun kara gurgunta halin da kasar ta Yemen ke ciki.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwarsa game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da hare-haren da aka kai a kusa da tashar ruwan Ras Issa.
Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya bayyana a wata sanarwa jiya Asabar cewa, “Guterres ya damu matuka da hare-haren da Amurka ta kai a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu a ciki da wajen tashar jiragen ruwa na Ras Issa na kasar Yemen, wanda ya yi sanadin jikkatar fararen hula da dama, ciki har da ma’aikatan agaji biyar.