Aminiya:
2025-04-03@18:34:33 GMT

Seaman Abbas da Hussaina: An dakatar da shirin Brekete Family Hausa

Published: 31st, January 2025 GMT

Rikici ya ɓarke tsakanin Seaman Abbas da matarsa Hussaina, da kuma mai gabatar da shirin nan na Brekete Family, Ahmad Isa da aka fi sani da Ordinary President.

Rikicin ya fara ne bayan Hussaina ta fitar da wani bidiyo tana cewa mijinta na yi mata duka, saboda zargin ta da yake da sama da faɗi da wasu kuɗaɗe da mota da aka ba su a matsayin tallafi.

A bidiyon ta kuma bayyana cewa tsangwamar ba ga iya shi ta tsaya ba, har na danginsa, abin da ta ce ya yi sanadiyar komawarta gidan iyayenta.

To sai dai mijin nata ya fito ya musanta zarge-zargen, inda ya ce suna zaune lafiya, hasali ma ta je ganin gida ne bayan rashin lafiyar da ta yi.

An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zina Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’a

Shi ma dai Ordinary President da ake zargin ya hana su Seaman ɗin tallafin Naira Miliyan 20 da Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya ba su, ya ce zance ne mara tushe balle makama.

Ya bayyana cewa a sakamakon waɗannan rikice-rikicen da suke ɓullowa a lamarin Usaina, ya daina gabatar da shirin Brekete Family da harshen Hausa.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’ar
  • Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin
  • Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano
  • Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Ta Bayyana Matsayinta A Shirin Makamashin Nukliya Na Kasar
  • Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
  • Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa 
  • Galadiman Kano Abbas Sunusi ya rasu
  • Ana Zaman Dar-dar A Kasar Zimbabwe Saboda Shirin Zanga-zangar Tsofaffin Sojaji