Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai Jigawa
Published: 31st, January 2025 GMT
Wata tankar mai cike da fetur ta yi bindiga a cikin wani gidan mai da ke garin Dutse, hedikwatar Jihar Jigawa.
A safiyar Juma’a ne kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Shiisu Adamu, ya sanar cewa lamarin ya faru ne a gidan mai na Shakkato da ke kan hanyar Kiyawa.
Hakan na zuwa ne yayin da aka samu karuwar fashewar tankoki dauke da man fetur a Najeriya, wanda mafi muninsu a baya-bayan nan ya yi ajalin sama da mutum 100 a Jihar Neja.
Ko a shekarar da ta gabata, irin haka ya faru a Jihar Jigawa, inda sama damutum 100 suka rasu.
Seaman Abbas da Hussaina: An dakatar da shirin Brekete Family Hausa An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zinaDa yake tabbatar cewa abin ya auku ne a ranar Alhamis, SP Shiisu Adamu ya bayyana cewa, amma ba a samu asarar rai ba.
Ya ce binciken farko ya nuna tankar man fetur din ta kama da wuta ne a yayin da motar take kokarin sauke man da ta dauko a gidan man.
“Kafin kiftawa da Bismillah wutar ta yi girma fiye da misali inda nan take aka kira hukumar kashe gobara, ta gaggauta zuwa tare da nasarar shawo kan lamarin.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jigawa tankar mai
এছাড়াও পড়ুন:
Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250
Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara.
Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya.
Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trnYayin bikin rabon dabinon, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da tallafa wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya.
Ya jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da taimaka wa Musulmai, musamman a lokacin watan Ramadan.
A bana, Saudiyya ta ware tan 50 na dabino don raba wa a Kano da wasu jihohin Arewa, baya ga tan 60 da aka riga aka aike Abuja a makon da ya gabata.
Ana ci gaba da shirin rabawa don tabbatar da cewa dukkanin kayan sun isa hannun buƙata.
Jakadan Saudiyya, ya kuma bayyana cewa shirin buɗa baki na ƙasar zai fara aiki ne a Abuja a ranar 3 ga watan Ramadan, inda za a raba wa Musulmai masu azumi abinci kyauta.
Ya kuma yi bayani kan irin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarkin ke yi a duniya, inda ya ce tuni cibiyar ta kammala sama da ayyuka 2,500 da darajarsu ta haura dala biliyan bakwai, waɗanda suka amfanar da ƙasashe 91.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Farouk, ya wakilta, ya nuna godiyarsa ga wannan kyauta.
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta tabbatar da cewa an raba dabinon ga waɗanda suka dace su amfana.