Nijeriya Na Da Dimbin Dukiyar Da Tinubu Zai Rika Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje – Minista
Published: 31st, January 2025 GMT
Da yake magana ta cikin shirin siyasa na talabijin Channels, ministan ya ce, shugaban kasa bai yi wasu tafiye-tafiyen da suka isa ba.
“Har yanzu wannan gwamnatin sabuwa ce. An rantsar da shi a 2023. Ta fuskancin duniya har yanzu shi sabon shugaban kasa ne. Yana bukatar tattaunawa da ganawa da takwarorinsa domin gina alaka mai kyau a tsakaninsu, sannan kuna iya ganin amfanun irin wadannan tafiye-tafiyen.
“Za ka sake tafiya ka samu zuba jari na dala biliyan 2 kamar yadda ya yi a Brazil. A zahiri, ba mu ma yi tafiye-tafiyen da suka isa ba. Ina ba da shawarar mu sake yin wasu karin tafiye-tafiyen.
“Nijeriya tana da dinbin dukiya. Nawa ne tafiyar zai lakume idan aka kwatanta da amfanin da hakan zai samar. Sannan, yanzu nawa ne ma kudin idan ka kwatanta da abubuwan da shugaban kasa ya riga ya shawo kansu.
“Nawa muke barnatarwa a tallafin mai, wutar lantarki da sauran tallafi,” ministan ya tambaya.
এছাড়াও পড়ুন:
YANZU-YANZU: Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kan Kisan Mafarauta A Uromi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp