Ko Jam’iyyun Adawa Na Iya Kai Bantensu A 2027?
Published: 31st, January 2025 GMT
A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari.
Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP, jam’iyyun adawa sun yi yunkuri da dama amma ba su samu nasara ba.
Kafin wannan, a shekarar 2018, jam’iyyar PDP ta kulla kawance da wasu jam’iyyun siyasa 38, inda suka sanya mata suna ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP) a wani taro da aka gudanar a cibiyar Musa Yar’adua da ke Abuja. Wannan gamayyar dai ta yi nufin kayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC a zaben 2019. Shugabannin jam’iyyun ADC, SDP, NCP, LP, da sauran jam’iyyu da dama da suka yi rajista sun halarci taron.
Sai dai kawancen ta kasa hana Buhari sake lashe zabe, saboda rashin kokarin habaka dimokuradiyya na samun goyon bayan ‘yan Nijeriya.
A ranar 6 ga Disamba, 2023, PDP, NNPP da wasu jam’iyyun siyasa biyar suka kafa sabuwar kawance. Jam’iyyun da abin ya shafa sun hada da ADC, APM, SDP, YPP da ZLP.
Wannan sabon yunkuri mai suna ‘Coalition of Concerned Political Parties’ (CCPP), an kafa shi ne a sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci jam’iyyun adawa da su hada kai a yunkurin kwace mulki daga hannun APC.
A ranar 12 ga Disamba, 2024, jam’iyyar PRP ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello ya tabbatar da tattaunawar a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban ADC, Ralph Nwosu a Abuja. Bello ya jaddada cewa, “Mun fara tattaunawa. Ba ma tsoron hadewa kwata-kwata. Jam’iyyar PRP ita ce jam’iyyar siyasa mafi dadewa a yau, kuma muna da tarihin kawance da suka samu nasara.”
Ana ta rade-radin cewa za a raba madafun iko tsakanin Atiku, Kwankwaso da Obi, inda Atiku zai yi mulki na tsawon shekaru hudu, sai kuma Kwankwaso na wasu shekaru hudu, da Obi na tsawon shekaru takwas. Sai dai a kwanakin baya Kwankwaso ya musanta wanzuwar irin wannan yarjejeniya, inda ya bayyana hakan a matsayin kage.
Shi ma ya musanta wata tattaunawa na hadewa ko yarjejeniyar siyasa da PDP, NNPP ko wata jam’iyya.
Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Jackson Lekan Ojo, ya yi imanin cewa jam’iyyun adawa za su iya kayar da Tinubu a 2027 idan suka yi amfani da dabaru irin na APC kafin zaben 2015. Ojo ya kara da cewa akwai batutuwa da dama a karkashin wannan gwamnati da ‘yan adawa za su iya cin gajiyarsu, da suka hada da kalubalen tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, da kuma cin hanci da rashawa.
“Idan har jam’iyyun adawa suka hada kai suka mayar da hankali kan gazawar gwamnati mai ci, musamman matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, za su iya samun nasara. Abu mai muhimmancin shi ne, a zakulo dan takara mai karfi wanda zai iya hada kan ‘yan adawa tare da gabatar da sahihin zabi,” in ji Ojo.
Daraktan makarantar nazarin zamantakewar siyasa ta Abuja, Dakta Sam Amadi ya yi imanin cewa hadewar jam’iyyun adawa za ta iya yin nasara idan har shugabannin ‘yan adawa suka kuduri aniyar cimma wata manufa ta ci gaban kasa tare da ajiye muradun kashin kai.
কীওয়ার্ড: tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato
Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato.
Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu.
Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman KanoRikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba.
Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar.
Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga Anguwan Rogo da Yantifa, waɗanda ke rikici da juna da daɗewa.
Duk da cewa har yanzu jama’a na cikin fargaba, Chizo ya tabbatar da cewa zaman lafiya ya wanzu a yankin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya kira taron gaggawa tsakanin shugabannin al’ummomin yankin domin kawo ƙarshen rikicin.
Wannan rikici ya faru ne kwana biyu bayan wani faɗa da ya ɓarke a harabar Masallacin Al-Mohap, inda aka kashe mutum uku daga cikin ‘yan Sara-Suka.