‘Yan Adawa Sun Caccaki Buhari Kan Kalamunsa Na Cewa, ‘Allah Ne Kadai Zai Iya Gyara Nijeriya’
Published: 31st, January 2025 GMT
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar.
Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya.
Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake nufi shi ne, muna cikin kasar da kafin sabon shugaban kasa ya hau kan karagar mulki ana tunanin zai yi garambawul. Abin takaici, idan har ya hau mulki ba ya iya aiwatar da komi.
“Kalamun Buhari ba shi da ma’ana a gare ni. Ba wani abu ba ne ma na so in yi magana a kansa saboda tsarin su ne. Kar ku manta wannan shugaban kasa na yanzu yana cikin wadanda suka yi zanga-zanga kuma suka yi yaki a NADECO domin gwamnati ta yi abin da ya dace. Amma a yau, sun kasa tsare ‘yan Nijeriya.”
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Ukraine Ya Sami Tarba Mai Kyau A Burtaniya Bayan Cacan Baki Mai Zafi Da Trump
Shugaban kasar Ukrain Volodomyr Zelesky ya samu tarba mai kyau a kasar Burtaniya bayan ya isa birnin London a jiya Asabar kuma bayan cacan baki mai zafi da yayi da shugaban Amurka Donal Trump a fadar White House dangane da yakin Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa shugaba Zeleski ya gana da firaiministan kasar Burtania Keir Starmer, wanda ya yaba masa kan yadda ya tsayawa kasarsa da kuma kasashen turai a gaban shugaban Amurka Donal Trump da mataimakinsa a ranar jumma’an da ta gabata.
Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zanta da shuwagabannin biyu, wato Trump da kuma Zeleski don kwantar da hankali.
A yau Lahadi ce za’a gudanar da taro na musamman kan abinda ya faru tsakanin Zelesky da Trump da kuma makoman kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da Rasha tun shekaru 3 da suka gabata.
Sauran shuwagabannin kasashen Turai sun yabawa Zelesky da yadda ya tsayawa kasarsa da kasa kasashen turai a tattaunawarsa mai zafi da manya-manyan Jami’an gwamnatin Amurka.