Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas
Published: 31st, January 2025 GMT
Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas.
Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan hanyarsu daga Barikin Myoung da ke yankin Marocco a Shomolu.
Waɗanda suka samu raunuka suna jinya a asibitin sojojin Nijeriya da ke Yaba, yayin da aka ajiye gawarwakin sojojin da suka rasu a ɗakin ajiye gawa a asibitin.
Hedikwatar Runduna ta 81 ta Sojojin Nijeriya, ta sanar a ranar Alhamis cewa za ta fara gudanar da tattakinta a yankin na farko, na kowace shekara a yau Juma’a.
Tattakin mai tsawon kilomita 15, wanda aka dakatar sakamakon wannan mummunan al’amari, ya kamata ya ratsa sassan babban yankin da tsibirin Legas.
Sanarwar ta kuma gargaɗi mazauna yankin da su kwantar da hankulan su domin tattakin da aka saba yi na atisayen soji ne.
Wata majiyar soji ta ce motar ta kutsa cikin taron sojojin, inda ta kashe wasu daga cikin su nan take.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, tun daga lokacin aka kama direban.
Sai dai majiyar ba ta bayyana inda ake tsare da mutumin domin amsa tambayoyi ba.
Wani ganau ya ce, “Tattakin hanyar ya tsaya kwatsam sakamakon lamarin. Ba zan iya bayar da cikakken bayani kan adadin waɗanda suka mutu ba, amma sojoji da dama sun samu munanan raunuka yayin da wasu ’yan ƙalilan suka mutu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yaba
এছাড়াও পড়ুন:
Motocin Buldoza Suna Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa a jiya Asabar ce motocin Buldoza na HKI suka shiga unguwar Almanshiya suka rusa gidajen wasu Falasdinawa, sannan suka bata hanyoyi a unguwar.
Kamfanin dillancin labaran Abadulu na kasar Turkiya ya nakalti Ashawish yana cewa, sojojin HKI su kan tilastawa Falasdinawa fita daga gidajensu sannan su rusasu a gabansu. Tare da umurnin su fice daga yankin su je inda suka ga dama.
Hamas ta kammala da cewa da wannan aikin zamu fahinci cewa gwamnatin HKI tana son kara korar Falasdinawa daga kasarsu, musamman daga yankin yamma da kogin Jordan.
Kungiyar ta bukaci MDD ta dauki matakan da suka dace don hana yahudawan mamayar karin gidajen Falasdinawa a arewacin yankin yamma da Kogin Jordan.
A jiya Asabar kwanaki 21 cur Kenan gwamnatin HKI take rurrusa gidaje da lalata hanyoyi a garuwan Falasdinawa dake yankin yamma da kogin Jordan musamman garuruwan Tulkaram, da Jenin.
Majiyar asbitoci a yankin yamma da kogon Jordan sun bayyana cewa daga lokacin zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 64 sannan wasu dubbai an koresu daga gidajensu.