An Fara Bukukuwan Kwanaki Goma Na Cin Nasarar Juyin Juya Halin Musulinci A Iran
Published: 31st, January 2025 GMT
Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga jirgin saman Air France da ya dawo da Imam Khumaini gida daga gudun hijira na sama da shekaru 14 wanda ya kai ga kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A yayin bukukuwan al’ummar Iran suna halartar taruka daban-daban har zuwa zagayowar ranar 22 ga watan Bahman wato 10 ga watan Fabrairu, wato ranar tunawa da juyin juya halin Musulunci.
Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai ya sake fasalin tsarin siyasar Iran ba ne, har ma ya sake fasalin matsayinsa na duniya, tare da kafa Jamhuriyar Musulunci a matsayin sabuwar hanyar samun ‘yancin kai daga wani yanki na gabas ko na yamma.
Ta hanyar kifar da gwamnatin sarki Shah Pahlavi shekaru 46 da suka gabata, al’ummar Iran sun kawo karshen mulkin shekaru 2,500 na sarauta tare da kafa wani sabon tsarin siyasa jamhuriya mai tushe bisa kimar Musulunci da dimokuradiyya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Rasha Ta Sanar Da Tsagaita Bude Wuta Da Ukraine Na Tsawon Kwanaki Bikin Ester
Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar.
Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”
Putin ya kuma jaddada cewa: A ko da yaushe Rasha a shirye take don warware rikicinta da Ukraine ta hanyar lumana, kuma tana maraba da muradin Amurka, China da sauran kasashe na ganin an cimma daidaito kan batun na Ukraine.