A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai.

Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen man da sauki daga gun matatun main a Dangote da kuma na MRS.

A cewarsa, a yanzu haka ‘ya’yan IPMAN na yin dakon man daga gun wadannan matatun biyu, ba tare da matatun sun yi masu karin farashin man ba, inda ya shawarci sauran ‘ya’yan kungiyar da su je su yi rijista da wadannan matatun, domin su rinka sawo man da sauki.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato

Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato.

Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi.

An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa

Wani ɗan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun da misalin ƙarfe 6:30 amma sai wurin ƙarfe 3:30 na rana aka samu nasarar kashe ta.

A cewarsa, gobarar ta yi ta’adi a ɓangaren shagunan masu sayar da abinci da suka haɗa da gero, dawa da masara da shinkafa.

Haka kuma, majiyar ta ce wutar ta yi ɓarna a ɓangaren masu ƙyamare da layin maƙera da masu maganin gargajiya.

“A ƙiyasi an yi asarar kuɗi za su kai Naira miliyan 500 domin dukkan shagunan da gobarar ta taɓa sun ƙone ƙurmus, masallaci ne kawai abun bai shafa ba.”

Ya buƙaci gwamnati da ta jingine batun siyasa a gefe wajen kafa kwamitocin da take ɗora wa alhakin bibiyar wannan ibtila’i domin ɗaukar matakan da suka dace bisa adalci.

Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku cikin ƙasa da shekara ɗaya da ake samun tashin gobara a kasuwar.

Ya nanata kiran cewa bayan jajanta wa ’yan kasuwa akwai kuma buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin kare dukiyar mutane daga irin wannan hasara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki
  • Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu ruwa da tsaki kan illar bautar da yara
  • Iran: Majalisar dokoki ta tsige ministan tattalin arziki saboda hauhawar farashi
  • Ta ina Kungiyar Hizbullah ke samun kuɗaɗenta?
  • An kama ɓarayin waya a Kano
  • Al-Houthi : Isra’ila Na fakewa Da Goyan Bayan Amurka Tana Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
  • HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato
  • Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa
  • A Yau Ce Dokar Haramta Amfani Da Tankunan Mai Masu Daukar Lita 60,000 A Najeriya
  • Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta ‘Euro-Med Monitor’ Ta Ce Ta Sami Shaidu Wadanda Suka Tabbatar Da Cewa HKI Tana Azabtar Da Fulasdinwa