Leadership News Hausa:
2025-04-03@02:37:35 GMT

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe N2.5bn A Auren Gata

Published: 31st, January 2025 GMT

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe N2.5bn A Auren Gata

Bugu da ƙari, Naira miliyan 267.6 an ware su domin shirye-shiryen Addinin Musulunci da tallafa wa waɗanda suka Musulunta, yayin da Naira miliyan 589 za a yi amfani da su wajen bincike kan harkokin tsaro da kuma yaƙi da bara a tituna.

Jimillar kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719.

75, wanda ya karu da kashi 31 daga asalin kuɗin da aka gabatar da farko, kuma ya fi na shekarar 2024 da kashi 65.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe

Game da aka yi wa mafarauta 16 a Udune Efandion, karamar hukumar Uromi ta jihar Edo, gwamna Monday Okpebholo ya yi kakkausar suka ga wannan aika-aika na rashin hankali, yana mai bayyana hakan a matsayin “wani abu da kuma muguwar dabi’a.

 

 

Okpebholo, tare da Gwamna Abdullahi Yusuf na Jihar Kano, sun yi addu’a ga rayukan wadanda abin ya shafa a kauyen Bunkure na jihar Kano inda wadanda abin ya shafa suka fita tare da kuma da bada tabbacin ga iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a gurfanar da masu laifin gaban kuliya.

 

Allah wadai da gwamnan ya biyo bayan harin da wasu gungun ’yan bindiga suka kai wa mafarautan, wadanda aka yi kuskuren cewa masu garkuwa da mutane ne, wanda ya yi sanadin kashe mutane 16.

 

 

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce, inda shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a farauto wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da umurtar jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa.

 

Okpebholo ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin an kamo duk wanda ke da hannu a harin tare da gurfanar da shi gaban kuliya. Ya zuwa yanzu dai an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a lamarin.

 

Gwamnan ya kuma yabawa al’ummar jihar Kano da ma daukacin yankin Arewa kan rashin daukar doka a hannunsu da sunan harin ramuwar gayya.

 

 

Ya sanar da cewa, ana shirin bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa.

 

Gwamna Yusuf wanda ya karbi bakuncin Okpebolo a Kano, ya yi alkawarin bayar da tallafin kudi da kayan abinci ga iyalan mafarauta da aka kashe a Uromi, jihar Edo.

 

 

Ya kuma yi alkawarin cewa za a biya diyya ga wadanda lamarin ya shafa, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

 

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Nijar, ta saki ministocin hambarariyar gwamnatin Bazoum
  • Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m
  • Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa
  • Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi 
  • HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
  • Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe
  • Abba Ya Nemi Gwamnatin Edo Ta Biya Diyyar Matafiyan Da Aka Kashe A Uromi
  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka