Gwamna Buni ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Tafkin Chadi
Published: 31st, January 2025 GMT
Gwamnonin tafkin Chadi da suka haɗa da Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, sun zaɓi gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin.
Sanarwar na cewar, an zaɓi Gwamna Buni ne a ranar Juma’a a ƙarshen taron ƙungiyar gwamnonin tafkin Chadi karo na 5 da aka gudanar a Maiduguri.
Tun farko shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne wanda mataimakin shugabansa Kashim Shettima ya wakilta ya bayyana buɗe taron da gwamnatin Jihar Yobe ta shirya.
Gwamna Buni a jawabinsa na karramawa ya yaba wa shugaba Tinubu bisa yadda ya samar da jagoranci ga ƙasa da yankin a cikin mawuyacin hali.
Ya gode wa takwarorinsa Gwamnonin yankin tafkin Chadi, da wakilai da sauran masu ruwa da tsaki saboda halartar taron da kuma bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar taron.
“Ina miƙa godiya ta ga mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa jagorancinsa da jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya da tsaro da ci gaban yankin tafkin Chadi.”
“Ina da yaƙinin cewa, mun sanya zamanmu a nan a cikin ‘yan kwanakin nan ya zama abin tunawa da albarka tare da yin adalci a kan taken taron “Sake gina tafkin Chadi: Ƙarfafa Ci gaban yankin, sadaukar da kai ga zaman lafiya, haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin, tsaro da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar yankin.” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana fatansa yana mai cewa “a matsayina na mai masaukin baki ina fatan za mu aiwatar da dukkan darussa da ƙudurorin wannan taro don ci gaban wannan yanki.
“Saboda haka, muna sa ran samun ƙarin haɗin gwiwa, tallafi da rabon albarkatun da ake buƙata don aiwatar da burinmu na gina kyakkyawan yanki mai wadata ga jama’armu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi
এছাড়াও পড়ুন:
Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron.
Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a kokarin da kwamitin ya yi na kiyaye muhalli. Dole ne a nace ga jagorancin da JKS ta bayar a wannan bangare, da ma sauke nauyin dake wuyan hukumomin wurare daban-daban karkashinta.
Taron ya kuma jadadda cewa, ya kamata a kara karfin sa ido a siyasance, da mai da hankali kan yadda ake tabbatar da manufofi da tsare-tsaren kwamitin, ta yadda za a ba da tabbaci ga aikin zamanintar da al’ummar Sinawa yadda ya kamata. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp