Gwamnatin Tarayya Da Kasar Faransa Sun Sake Sabunta Yarjeniyar Farfado Da Hakar Ma’adanai
Published: 31st, January 2025 GMT
A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu.
Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar.
Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata ayi, domin a cire dukkanin wani kwankwato da ake da shi, musamman domin a samar da samakon da ya kamata.
Shi kuwa Farfesa Olusegun Ige, Darakta Janar na Hukumar ta NGSA ya sanar da burin Hukumarsa na son samun kayan kimiyyar zaman, domin ta kara bunkasa ayyukanta, inda ya yi nuni da cewa, rashin samun kayan aikin na fasahar zamani, na janyo jinkiri wajen gudanar da ayyukan hakara Ma’adanai masu dimbin yawa a kasar nan.
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Nanata Adawa Da Matakan Tilastawa Da Nuna Babakeren Tattalin Arziki
Ya ce, bisa tagomashin katafariyar kasuwarta, da kyawawan manufofin da ake tsammani, da ingantaccen yanayin kasuwanci, Sin na ci gaba da zama kasa mai albarka ga kamfanonin kasa da kasa su zo su zuba jari domin samun bunkasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp