Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar hankali.

Yayin bikin, hukumomin kula da layin dogo na sassan kasar sun kara karfin aiki a wuraren da aka fi amfani da su, da inganta karfin ba da hidimmomin jiragen kasa da tashoshi, da aiwatar da matakan saukakawa jama’a, da kuma kokarin samar wa fasinjoji ingantacciyar hanyar tafiya.

Alal misali, reshen Beijing na kamfanin kula da layin dogo na kasar Sin, ya kara tashoshin caji a tashar jiragen kasa ta yammacin Beijing don biyan bukatun fasinjoji na cajin na’urorin lantarki. Shi kuwa reshen Chengdu na kamfanin layin dogo na kasar Sin, ya kafa tashoshin kulawa da kofofin shiga da wuraren binciken tsaro dake cikin manyan tashoshin jiragen kasa a birane 53, ciki har da tashar gabashin Chengdu da tashar arewacin Chongqing, don ba da fifiko ga fasinjoji na gaggawa da fasinjoji masu rauni kamar tsofaffi, yara, marasa lafiya, nakasassu da mata masu juna biyu cikin mintuna 15 kafin jirgi ya tashi. A Urumqi kuwa, kamfanin layin dogo na kasar Sin ya sanya akwatunan ba da hidimomi a jiragen kasa, wadanda suke samar da abubuwa kamar kayayyakin hana sauraron sauti ta kunne da marufin ido da ba za a iya sake amfani da su ba.(Safiyah Ma)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: layin dogo na jiragen kasa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugabar Tanzaniya Ta Yaba Da Yadda Ake Ci Gaba Da Samun Karuwar Jigilar Kayayyaki A Tashar Tanga Da Sin Ta Inganta

Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara.

“Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa Hassan a jawabinta ga kasar a karshen ziyararta a yankin Tanga. Tana mai cewa, babban kamfanin gine-gine mallakin kasar Sin wato China Harbor Engineering Compnay, shi ne ya yi aikin inganta tashar ta Tanga. Ta kara da cewa, inganta tashar da aka yi ya kuma samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da shirye-shiryen mayar da tashar ta zama cibiyar jigilar takin zamani da kayayyakin noma. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwance Damarar Dakarun Hashdu Zai Ragewa Harkokin Tsaron Kasar Iraki Aminci
  • Masana Fasahar Gina Jiragen Sama A Iran Sun Samar Da Wata Fasahar Nano Mai Rage Nauyin Jiragen Sama
  • An Yi Jana’izar Shugaban Kasar Namibia Da Ya Samo Mata ‘Yanci
  • Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo
  • Shugabar Tanzaniya Ta Yaba Da Yadda Ake Ci Gaba Da Samun Karuwar Jigilar Kayayyaki A Tashar Tanga Da Sin Ta Inganta
  • Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila
  • Noman Rani: Tinubu Ya Amince Da Fadada Madatsun Ruwa 12 A Nijeriya
  • Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
  • Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu
  • Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa