Sin Ta Mayar Da Martani Ga Shirin Japan Na Aiwatar Da Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Sin
Published: 1st, February 2025 GMT
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da shirin Japan na aiwatar da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa Sin, ciki har da semiconductor.
Kakakin ya bayyana cewa, shirin bangaren Japan na aiwatar da matakan, zai kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na tsarin masana’antu, da gurgunta mu’amalar kasuwanci na yau da kullum dake tsakanin kamfanoni, da kuma lalata muradun kamfanonin kasashen biyu.
Sin na fatan kasar Japan za ta ji ra’ayoyin masana’antu, ta kuma gaggauta gyara ayyukan da ta yi bisa tushen kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da moriyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin.
Bugu da kari, ya ce kasar Sin za ta dauki matakan kiyaye hakki da moriyarta.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara
Sanata Abdul’aziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana shirin tallafa wa marayu 20,000 a faɗin Jihar Zamfara.
Yayin da yake magana bayan cin abincin Sallah tare da marayu 500 a gidansa da ke Talata Mafara, Sanata Yari ya ce an shafe watanni tara ana tantance marayun daga ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne za su amfana da shirin.
Abba Ya Nemi Gwamnatin Edo Ta Biya Diyyar Matafiyan Da Aka Kashe A Uromi Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTFYa bayyana cewa shirin tallafin wanda zai fara aiki kafin Idin Babbar Sallah, inda za a ware duk abin da marayun ke buƙata don kyautata rayuwarsu.
“Mun shirya wannan tallafi ne domin amfana da albarkar taimakon marayu, kamar yadda Alƙur’ani da Manzon Allah (SAW) suka hore mu,” in ji Sanata Yari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp