HausaTv:
2025-02-01@06:56:51 GMT

Kissoshin Rayuwa Imam Hassan (a) 09

Published: 1st, February 2025 GMT

09-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasan ce tare da mu.

///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na farko.

A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo banagre na ukku na hadisan manzon All..(s) wadanda suke magana kan matsayin iyalan gidansa a duniya da Lahiri, ya bayyana cewa a duniya ba wanda yake kan shiriya sai wanda yake tare dasu yake sonsu yake biyayya a garesu kuma ya mutu a kan hakan.

Sune kofar shiriya wanda ya bi ta wata kofa ba zai taba samun shiriya ba. Ya kwatantasu da jirgin annabi Nuhu(a), wanda ya shiga ya tsira wanda kuma yak i shiga tabbaza ya halaka. Babu wata hanyar tsira sai ta wajensu.

Mun kawo hadisi inda yake cewa ya barwa al-ummarsa nauyaya guda biyu, littafin All..da kuma iyalan gidansa, duk wanda ya rikesu su biyu zai tsira, duk wanda ya barsu, ya halaka. Yace All..T ya fada masa kan cewa ba zasu rabuba har su hadu da shi a tabkin alkauthara.

Har’ila yau mun bayyana cewa mujarradin sonsu a zuzciya bai wadatarba. Dole ne musulmi ya dauki ikidarsa, da ibadarsa da mu’amalarsa da halayensa daga karesu. Dole ne su zama abin koyi ga musulmi. A wannan halinne, wanda ya mutuna yana sonsu zai shiga aljanna, zai mutu wanda aka yiwa gafara, wanda aka karbi tubansa, sannan za’a kaishi aljanna kamar yadda ake zuwa da amarya dakin mijinta.

Daga karshe munji yadda aka yiwa manzon All..(s) Ishara da barinsa nan duniya, ta ayoyin alkur’ani mai girma, wadanda suka hada da (Kai mai mutuwa ne, kuma suma masu mutuwa ne} sannan da suratun Nasr., daga nan ya tabbatar da cewa kaurecewarsa daga nan Duniya ya ku sa.

Bayanda manzon All…(s) ya fahinci cewa tafiyarsa daga wannan duniya zuwa ganin lahira ta kusa tafiya wanda babu dawowa a cikinta, sannan ya san irin wahala da ya sha wajen ganin wannan addinin ya tabbata, har zuwa lokacinda mafi yawan kasashen larabawa suka mika kai addinin musulun ci sannan ya fahinci cewa manya manyan daulolin duniya a lokacin wata Farisa da Roma ta gabasa, ko bizantine, sun razana da samuwar wannan sabuwar daula kusa da su, sun fara shirye-shiryen mukusheshi, tun bai ya karfin da zai gagaresu ba. Kuma daular Roma ta gabas ta taba yaki da rundunar musulmi sau guda kafin wafatinsa, inda a shekara ta 8 bayan hijira, ya tura dan amminsa Ja’afar dan Abitalib (a) da zaidu bin Haritha da kuma Abdullahi bin Rawah zuwa da runduna mai mayaki kimani 3000, inda suka kara da rundunar roma ta gabasa wadanda suke da mayaki kimani 200,000, a wani wurin da ake kira Mutata a cikin kasar Jordan a halin yanzu. Don haka yana da masayiya kan cewa akwai fafatawa a tsakaninsu nan gaba.

Tare da wannan duka, sai manzon All..(s) ya farra shirin ganin wannan daular ta tabbata a bayansa. Ta kuma sami nasara a kan wadannan manya-manyan daulolin a bayansa, ba tare da wannan wata matsala ba.

Don haka sai yi kirra dukkan musulman da zasu iya zuwa hajjan shekara ta 10 bayan hajira, wannan ake kira hijjatul Isalam ko hajjin musulunci, ko kuma hajjin bankwana, don manzon All..(s) bai boyewa kowa ba kan cewa wannan hajjin shene hakkin bankwana, wato daga bayan hajjin kafin hakki na gaba baya duniya.

Don haka yana daga cikin abinda yake fada masu a khudubi da ya gabatar masu, Yace: “Lallai ni ban sani ba, mai yuwa ba zan sake haduwa da ku bayan wannan shekarar ba….”     

Don haka yak ira dukkan musulmi wanda zai iya a halarci hajjin ban kwana, ko w aya sani, wannan hajjin ba don ya nuna basu ayyukan ibada na Hajji kadai ba, sai dai daga cikin muhimman al-amarin da ya shaida masu a wannan hajjin tun daga ranar da ya shiga Makka har zuwa karshen hajji da kuma bayansa shi ne, wadanda zasu shugabancesu a bayansa, don tabbatar da wannan daukakar ta musulin da kuma kasancewarsu a kan tafarki na gaskiya.

A cikin daya daga cikin khudubobinsa yana cewa{Ya ku mutane, lalle ni na bar nauyaya biyu a cikin ku, littafin All..da kuma zurriyata, Ahlubaiti na,… }.

A nan kamar yadda zaku gani, yakan hada zurriyarsa da Ahlubaitina, don ya san akwai wadanda suke sanya matansa a cikin iyalan gidansa, amma idan ya ce, zurrriyyata, ta matansa basa shiga cikin zurriyarsa, yayansa kawait suke iya daukar wannan shifar.

A wasu hadinsa kamar yadda muka karanta a shirye-shiryemmu na baya, yana gwama Zuriiyarsa da alkur’ani mai girma, sanan ya sanya riko da su, tare ne zai tsiratar, riko da daya daga cikinsu ba zai zama tsira ba.

Da a ce al-ummarta ta bi zancensa, a cikin wannan maganar da bata fada cikin musibu, da wahalhalu, da kaskanci da wulakanci ba su samesu a bayansa ba. Da al-ummarsa basu yi sabani a tsakaninsu ba, da bata rarraba ta zama kungiyoyi daban daban, wadanda suke kafirta juna a tsakaninsu ba. Ko wace kungiya tana alfahira da mabiyanta tana kuma fadin cewa itace kadai hanyar tsira ba.

A hajjin bankwana dai manzon All…(s) ya yi khudubobi har guda 3-5, a zancen wasu malaman. Amma khuduba mafi muhimmanci itace wacce yayi a wani wuri da ake kira Ghadir Khom, tsakanin Makka da Juhfah, inda ya tsaida su, a cikin tsakiyar Rana, kafin azahar, wadanda suka yi gaba da shi ya sa aka kirasu suka dawo, sannan ya jira wadanda suke baya suka riske shi.

Don haka wannan khudubar ba a cikin lokacin Hajji aka yi ta ba, sai dai yayita ne a ranar 18 ga watan Zulhajji, kwanaki 7 ko 8 bayan sallah babba.

Me yasa bai yita a ranar Arfa a gaban dukkan musulmin da suka halarci aikin hajji ba, ? sai mu ce ya fadeta a rannar, amma ba tare da ayyana sunan Aliyu dan Abitalib (a) a matsayin shugaba a bayansa ba. Sai dai ya ambaci iyalan gidansa, da kuma Alkur’ani kamar yadda yayi a sauran hudubobin. Idan da ya tsaya hakamma da ya wadatar, to amma All..T yana son ya fidda sunan Aliyu dan Abi talib a gaban Jama’a , shi yasa ya sauko da aya ta musamman a cikin suratul Ma’aida, inda yarfafa masa, magana, kan cewa idan har bai yi hakan ba, to kuwa duk aikin shekaru 23 da yayi yana isar da sakon All..ta kamar bai yi su ba.

Ayar tana cewa

{Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.}  Alma’ida 67.

Wannan ayar ta sauka ne a wannan wurin a lokacinda manzon All..(s) yana kan hanyarsa ta komawa madina bayan – kammala aikin Hajji- a lokacinda ya isa wannan wurin sai Mala’ika jibrilu ya sauko masa da wannan ayar, tare da umurnin ya tsaya a wurin ya nada Aliyu dan Abitalin da sunansa a matsayin khalifansa a bayansa.

Kuma bayan ya nadashi, ya zauna kwanaki uku a wurin dukkan sahabban manzon All..(s) wadanda suke wurin suka yi masa bai’a, kan cewa shine khalifar manzon All..(s) a bayan wafatinsa. Sannan umurnin All..T a wannan karon kamar yadda ya zo cikin karshen ayar , shi ne ya nada Aliyu a matsayin khalifansa a bayansa, ko menene girman hatsarin da yake ganin hakan zai jawo, don All..zai isammasa, daga sharrin wadanda basu amince da haka a cikin mutane ba. 

Malaman tarihin sun bayyana cewa tsakanin nada Aliyu (a) a matsayin khalifan manzon All..(s) da wafatinsa (s) kwanaki 70 ne kacal.

Har’ila yau wannan ayar za zo masa (s) kamar gargadine a wajen All..T kan cewa, idan har bai isar da wannan sakon guda ba, to yana dai dai da cewa dukkan wahalarsa da kokarinsa na shekaru 23 tun tafi a banza, don All…ya dauke shi kamar bai isar da sakonsa ba.

A nan manzon All..(s) yayi sallar Azzahar da su a cikin tsananin rana, (yin hakan yana da hikimarsa, don yana iya cewa su isa Jufa tunda gari ne ya tsaya cikin inuwa suma su sami inuwa sai yayi khudubarsa, amma sai ya tsaya a inda ayar ta sauka, sannan mutane suna saya rigunansu a kasar kafafuwansu saboda zafin kasa, ga kuma rana a sama) sannan ya buaci a sanya masa sirduna da haudaju na dabbobinsu a matsayin mimbari sannan ya hau yayi khudubarsa ta Ghadie. Wasu malamai sun bayyana khudunar Ghadir itace khuduba mafi tsawo a dukkanin khubobin manzon All..(s)..

Don haka manzon All..(s) ya tashi a Ghadir Khom ya yi khuba mai tsawon gaske, inda a cikinta ya kawo dukkan cika- cikan imani, yar da All..abinda bauta sai shi kadai, imani da shi a matsayin manzo, yarda da wuta da aljanna gaskiya ce, sannan sai yace {..Duk wanda ni shugabansa ne, to wannan Aliyun shugabansa ne…}.

Malaman tarihin sun yi sabani kan yawan mutanen da suke tare da shi a lokacin, wasu sun ce 100,000 wasu sun ce fiye da haka. Kawo ya san cewa mutanen da suka je aikin Hajji sun fi haka, don haka bayan a kammala Hajji, ba kowa ne ya kama hanyar Madina tareda manzon All..(s). Misali mutanen Yemen sun kama hanyar kasarsu hakama mutanen iraki sun kama hanyar su. Wadanda suka tare da manzon All..(s) wadanda suke zuwa madina ko kan hanyar madina ne suke tare da shi (s).

Kuma bayan duk wasu jumloli, sai yace masu, na isar da sako sai suce, ka isar, sai yace All..ka shaida.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu, wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: iyalan gidansa wadanda suka wadanda suke masu sauraro kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba

Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba.

 

“Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama.

 

“Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.”

 

Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don kauce wa irin waɗannan haɗurran.

 

Haka kuma, ministan ya jaddada damuwar Shugaban Ƙasa kan yawaitar irin waɗannan bala’o’i a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa dole ne a ƙara wayar da kan al’umma domin daƙile aukuwar irin su a nan gaba.

 

Ya ce: “Abu na farko da ya kamata mu gane shi ne irin wannan bala’i yana faruwa sau da yawa a ƙasar mu, kuma Shugaban Ƙasa yana cikin matsanancin baƙin ciki. Ya kuma umarta cewa Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ta gudanar da wayar da kai da faɗakarwa, musamman a cikin waɗannan ƙauyuka, domin hana aukuwar irin hakan a nan gaba.”

 

A ƙarshe, Idris ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Neja ta yi wajen ɗaukar matakin gaggawa game da lamarin, tare da bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci tare da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Limamin Juma’ar Tehran Ya Jinjinawa Wanda Ya Assasa Juyin Musuluncin A Iran Marigayi Imam Khumaini ( R.A)
  • Kisoshin Rayuwa: Imam AlHassan (a)
  • Badakala: Bankin Duniya Ya Kakaba Wa Kamfanoni 2 A Nijeriya Takunkumi
  • Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
  • Kadan Daga Hakuri Da Yafiya Da Rangwamen Annabi (SAW)
  • Cece-kuce Ya Barke Kan Shirin “Kur’anic Convention”
  • JMI Ta Cika Shekaru 46 Cib Da Nasarrar Juyin Juya Halin Mususlunci A Kasar, Wani Irin Ci gaba Ne Ta Samu A Cikin Wannan Lokacin
  • Tsohon Shugaban Google: Deepseek Ya Kawo Muhimmin Sauyi A Bangaren AI
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Zata Kalubalanci Duk Wanda Ya Kai Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyarta