Kisoshin Rayuwa: Imam AlHassan (a)
Published: 1st, February 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi.
///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na farko.
A cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar cewa bayan da manzon All..(s) ya tabbatar da cewa wafatinsa ya kusa, ta hanyar ayoyin da suka sauko masa, wadanda suka hada ta Suratun-Nasr, sai ya fara tunanin al-ummarsa a bayansa.
Bayan dukkan wahalhalun da ya sha, har zuwa lokacin da mafi yawan kasashen larabawa suka karbi addinin musulunci, duk da cewa wasu sun sallama ne, amma imani bai shiga zuciyarsu ba, kamar yadda All..ya bayyana a cikin alkur’ani mai girma.
Amma da ya fahinci cewa wafatinsa(s) ya kusa, sai ya kira musulmi gaba daya, wadanda suke da ikon zuwa su je aikin hajji tare da shi, to su fita. A dukkan khubobin da yayi, sai ya fada masu cewa, wannan itace shekara ta karshe gareni a nan duniya, mai yuwa ba zamu sake haduwa da ku ba. Amma ina bari nauyaya guda biyu, alkur’ani mai girma, da kuma iyalan gidana, zurriyata, Ahlubaiti ba, da sauransu.
Yayi khuduba a ranar arafah inda ya ce masu kada ku zama kafirai a bayana sashenku yana dukan wuyan sace, sannan ya ce nanata masu riko da alkur’ani da kuma iyalan gidansa.
Amma a khubarsa ta karshe wanda ta kasance a Alhamis 18 ga watan Zulhajji a wani wuri tsakanin Makka da Jufah, wanda ake kira Ghadir Khum.
Mun bayyana cewa aya ta 67 na suratul Ma’ida ta sauka ta umurceshi da ya isar da sakon All..idan kuma baiyi ba to kamar bai iasar da sakonsa gaba da ya ba, sai ya tsaya nan take, aka yi masa mimbari ya hau ya kuma yi khuduba mai tsawo inda a cikinta ya kawo cika-cikan imani, gaba dayansu. Sannan yayi khudubar ya kammala inda kafin ya kammala ya daga hannun Aliyu (..wanda ni shugabansa ne to wannan Aliyun shugabansa ne).
Da wannan khuduba ta gadir ce manzon All..ya kammala isar da sakon All.., sannan bayan wannan bikin na nada Aliyu dan Abitaklib (a) a matsayin sai All..T ya sake aika mala’ika Jibruli ya tabbatar masa cewa ya isar da sakonsa, kuma da wannan sakon All..ya kammala addininsa, ya kuma cika ni’imarsa a kan al-ummar musulmi ya kuma yarje masu addinin musulunci ya zama addini. Kamar yadda ya zo a cikin wannan yar itama a cikin surarul Ma’ida inda All..yake cewa
{… A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni’imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. …}
Amma ita khudubar ghadir me ta kunsa, kuma da wani tsari manzon All..(s) ya gabatar da ita.
Da farko bayan ambaton sunan All..ya yabonsa kamar yadda ya saba a khudubobinsa, sai ya kawo masu irin ni’iman da All..yayi masu na aiko shi da kuma yadda ya sha wahala wajen bayyana masu gaskiya, da kuma kubutar da su daga bautar gumaka, sannan ya mabici, wasu hukunce-hukuncen sharia da ladubba wadanda ya bukace su su aiwatar da shi a cikin rayuwarsu.
Daga baya, yazo kan cikekken abinda yake son fada a khudubatsa. Sau yace masu {Ku dubi yadda zaku kula da nauyaya biyu da zan bari a cikinku}. Sai wani daga cikinsu ya daga murya yace: Menee Thaqlaini ya manzon All..), sai ya amsa masa da cewa: Nauyi babban shi ne Littafin All…(kamar igiya ce) dayan bangaren na hannun All…mai girma da daukaka, sannan dayan bagaren kuma yana hannunku, ku yi riko da shi ba zaku bata ba.
Sannan dayan kuma (wato nauyi na biyu) shi ne karami, zurriyata. Hakika,(All..T) mai ludufi kuma masani ya fada mani cewa su biyu din nan ba zasu rabu ba har sais un riskeni a taki, kuma na roki Ubangijina kan hakan, kada ku yi gaba da su ku halaka, kada kuma ku yi baya da su ku halaka,
Sannan ya kama hannun Aliyu (s), ya daga, har sai da hasken hamarsu ya bayyana, kuma kowa daga cikin mutane suka gano shi, sannan sai yace: Ya ku mutane, wa yafi cancanta da muminai a kan kawokansu, sai suka ce: All..da manzonsa ne suka sani. Sai manzon All..(s) yace: Lalle All..shi ne shugabana, ni kuma nine shugaban muminai, Kuma ni nafi cancanta da su kan kawukansu, To wanda na kasance shugabansa, to Aliyu shugabansa ne, ya maita hakan har sau ukku, ko kuma har sau hudu.
Sannan yace : Ya ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi ka yi adawa da wanda yake adawa da shi, ka so wanda ya so shi, ka kuma ki wanda ya kishi, ka taimakawa wanda ya taimaka masa, ka taabar da wanda ya taabar da shi, ka jujjuya gaskiya tare da shi , ta duk inda gaskiyar ta juya. Ku saurar, Lallewanda ya ji isarwa baya nan. ! ».
A lokacinda manzon All..(s) ya kammala khudubarsa, mau daukaka, wanda ya cikata da girmama amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), da kuma dora masa, khallifanci mafi girma, sai Haasan Dan Thabit ya tashi zuwa wajen manzon All..(s), inda ya nemi izininsa na tsara wasu baitoci, don don ambatun wannan manasaba, ko al-amari mai girma da ya faru a wannan ranar, sai yayi masa izini. Sai hassan ya tashi a cikin mutane yana cewa :
Annabinsu yana kiransu a ranar Gadiri-A Khummin, kuma ka saurarri manzon Yana Kira
Sai yace waye shugabanku kuma annabinku-Sai suka ce, basu bayyana Rashin saninsani ba a lokacin.
Ubangojinka shugabammu kuma kaine annabimmu-Ba zaka tarar da masu saba maka ranar kiyama masu saba maka a shugabanci ba-Duk wanda na kasance shugabansa to wannan shugabansa ne-Ku kasance masa mabiya na gaskiya masu bi
A nan sai ya roki Ubangiji, ya jibinci Majibancinsa-Kuma ka kasance makiyin ga wanda yaki Ali.
Sai daga nan musulmi daban-daban suna ta zuwa suna masa mubaya’a, kan khalifanci, suna masa barka-barka, da zama shugaban muminai. Manzon All..(s) ya umurci dukkan matansa ‘Ummahatul Muminin su 9, su wajensa su taya shi murna, Umar dan Khaddabi yana daga cikin wadanda suka bashi hannu, yana cewa: Murna gareka ya kai Dan Abitalib ka kasance shugaba na, kuma shugaban dukkan muminai…
Sannan a wannan rana mai albarka ne, wannan ayar ta sauka, tana cewa
{A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni’imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku} Alma’idah 03.
Hakika ni’imar All…babba ta tabbata, kuma addini ya cika, tareda shugabancin Amirul muminina kuma shugaban masu tsoron All….
Manzon All..(s) ya tabbatar da mataki na karshe, don kare al-ummar musulmi, da kuma shari’ar musulunci, bai bar mutane cikin dimwa, wacce wacce zata jefasu cikin rudu basu san wa yakama, ko ya zama dole su bi shi ba. Sai dai ya nada masu mai shiriyatar da su zuwa hanya madaidaiciya.
Lalle, bai’ar Ghadir tana daga ciki, dalilai masu inganci, kuma wanda yake mafi bayyanar dalili na tabbatar da cewa Khalifanci, da shugabanci bayan manzon All..(s) ta Imam Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Shugabanci a bayan manzon All…(s) ta kebanta a gareshi shi kadai.
Kuma Imam Hassan (a) bayan shahadar mahaifinsa, ya kafa hujjar cewa shugabanci nashi ne bayan mahaifinsa.
Yayi haka ne a cikin khudubar da Imam Hassan (a) yayi bayan sulhun da yayi da mu’awiya dan Abu sufyan, inda yake cewa :
Mu Ahlul Bait, All..ya girmamamu da addinin musulunci, ya zabemu ya kuma sake zabemmu, ya tafiyar da dauda daga garemu, Ya kuma tsarkakemu tsarkakewa. Kuma mutane ba zasu rabuba sai All..ya sanya mu a cikin mafi alkhairinsu. Wannan daga annabi Adama har zuwa Kakana muhammad (s).
A lokacinda ya aiki shi tare da annabci, ya kuma zabeshi da manzznci, ya sauko masa da littafi, sannan ya umurceshi da kira zuwa ga All..mai girma da daukaka, babana ya kasance na farko wanda ya amsa kira ga All..da manzonsa. Shi ne na farko wanda ya yi imani sannan gaskata All..da manzonsa (s).
Hakki All..ya fada a cikin littafinsa da ya saukar ga annabinsa manzo. {Shin wanda yake kan bayyanennen Al-amari daga Ubanginsa, sannan wani mai shaida daga gareshi ya bishi}. Kakana shi ne wanda yake ban baiyanennen al-amari daga ubangijinsa, kuma babana ne ya bishi kuma shi ne mai shaida daga wajensa….har zuwa inda yace.. Hakika wannan al-ummar ta ji kakana, yana fada masu yana fada : Alumma ba zata shugabantar da wani mutum a cikin ta ba, alhali akwai wanda ya fi shi ilmi ba, sai al-amarinsu ya kasance yana yin kasa-kasa, har sais un koma zuwa ga inda suka bari.
Kuma sun ji shi yana fadawa babana : Matsayinka da ni kamar matsayin Haruna da Musa,sai dai kawai babu annabi a bayana, kuma hakaki sun ganshi, kuma sun ji shi a lokacinda ya riki hannun babana a Ghadir Khum, ya fada masu : Duk wanda na kasance shugabansa ne to Aliyu shugabansa ne.
Ya Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi, ka tabar da wannan ya tabar da shi, sannan ya umurcesu da isar da shi ga wanda baya nan.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: masu sauraro wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Badakala: Bankin Duniya Ya Kakaba Wa Kamfanoni 2 A Nijeriya Takunkumi
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Kamfanin na Biba Atlantic da Didam, sun sana son ra’ayin a cikin wasikar su ta samun umarni tare da samun bayanan sirri, daga gun ma’aikata, ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya ba su dama tabka badakala da aikata cin hanci da rasahawa.
Kazakla, sanarwar ta bayyana cewa, daga cikin yarjejeniyar, kamfanonin na Biba Atlantic Limited da Technology House Limited da kuma Didam, sun amsa laifinsu da kuma zubar da kimarsu.
Sanarwar ta bayyana cewa, wasu daga cikin abubuwan da ake bukatar Kamfanonin da kuma Didam da ake son su cika sharudda dole ne su bi ka’idar samun haro, kuma wajbi ne, su karfafa kimar bin ka’idar tsare-tsaren su.
Bugu da kari, dole ne wanzar ka’idar samun haro na shirye-shiryen su dai da da ka’idojin da Bankin Duniya, ya gindaya.