HausaTv:
2025-02-01@08:58:56 GMT

Duniyarmu A Yau: Ranar Basirah: 9TH Day A Wajen JMI

Published: 1st, February 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi.

Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?.

A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda yayi dai dai 29 ga watan Decemba na ko wace shekara yana da matukar muhimanci a nan JMI, Iraniyawa suna kiran ranar da ranar (basira). Ko kuma ranar da mutanen kasar Iran suka tabbatar da goyon bayansu ga jagoran juyin juya halin muslunci a kasar.

An gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Yunin shekara ta 2009, inda shugaban mai ci a lokacin Dr Ahmadi Najad da kuma, abokan hamayansa wadanda suka hada da Mir Hussain Musawi da Kuma Mahdi Karubi, da wani dan takaran suka cika ya Takara 4 masu neman kujeran shugaban kasa.

Bayan an fidda sakamakon zabe, sai gashi Dr Ahmadi Najad ya lashe zaben a zagaye na farko, hukumar zabe ta tabbatar da ingancin Zaben.

Amma yan Takara biyu, Mir Hussain Musawi wanda ya zo na biyu a zaben, da kuma Mahdi Karubi, sun fito a gaban kafafen yada labarai sun bayyana cewa basu yarda da sakamakon zaben ba. Kuma suna ganin an yi maguna a cikinsa.

Banda haka maimakon su je wajen hukumomin da abin ya shada don su cigar da korafinsu, sai suka tare mutane a cikin birnin Tehran suna jawabai wadanda suke tunzura mutane kan halaccin gwamnatin JMI gaba dayanta.

Dubban mutanen sun amsa kiransu a nan birnin Tehran da kuma wasu manya manyan birane a kasar wadanda suka hada da birnin Esfahan daya daga cikin manya-manyan birana a nan Iran.

Banda haka gwamnatin ta tura yansanda wadanda basa dauke da makami don tarwatsa su, amma al-amarin ya kara rincabewa a lokacinda masu zanga zanga suka fara kashe yansanda suna kona motocinsu suna kuma ababen hawansu.

Banda haka rigimar ta kai ga masu zanga zangar, wanda a halin yanzu ba inganci ko rashin ingancin zabe ba. Sai dai zanga zangar ta rikede ta zama da nuna kiyayya ga JMI da kuma zagin shuwagabanni mu samman jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khamina’ee.

Masu zanga zanga sun yi ta yayyaga dukkan hotunansa a kan titunan kasar.

Amma kamar yadda kowa ya sani kasashen yamma wadanda suke makirce-makircen ganin bayan JMI tun Randa aka kafata, sun sami damar da suke nema na ruruta wannan fitiyar mai yuwa su sami abinda suke nema fiye shekaru 30 a lokacin.

Don haka kasashen yamma sun yayata wannan zanga zangar, wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma da kuma wadanda suke goyon bayansu a yanking abas ta tsakiya musamman na kasashen larabawa sun yanke dukkan shirye-shryensu da suka saba suna nuna abinda yake faruwa a Iran, wanda kuma a fatansu zasu kawo karshen JMI.

Amma kwanaki na kara tafiya magoya bayan masu zanga -zangar na kara raguwa, amma dai suna fita a cikin daruruwansu a wurare daban-daban a cikin birnin Tehran da kuma wasu birane.

Amma rashin sa’ar da suka yi shi ne an gudanar da wadannan zanga -zanga ne a cikin ranakun farkon Muharram, wato kwanatin da Iraniyawa Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) suke kuka don shahadar Imam Hussain(s) jikan manzon All..(s) a wani wuri da ake kira karbala, a kasar Iraki a shekara ta 61 bayan hijira.

Banda haka masu-zanga zanga sun kai ga suna kona masallatai da huseniyoyi, tare da su har da alkur’ani mai girama. Wannan banda kayakin Jama’a da suka kona, wadanda suka hada da motocin BRT da bankunan da sauransu.

A nan ne sai reshe ta juye da mujiya, wato a ranar 9 ga watan Day, wato watan 10 a cikin kalandar Iraniyawa, miliyoyinn mutane a nan Tehran da kuma sauran biranen Iran suka fito kan tituna suna allawadai da masu zanga-zanga suna kuma bayyana goyon bayansu ga JMI da kuma jagoranta Imam Sayyid Aliyul Khaminaee.

Daga nan sai sauran masu tada fitina da sunan zabe suka bace a kan titunan, suka shige cikin gidajensu da lunguna a cikin birane, bayan sun ga ambaliyan mutane masu goyon bayan JMI da kuma Jagoranta.

Da haka kuma suka suka kawo karshen rigimar wacce aka dau kwanaki ana yi, suka kawo karshen rigimar a rana guda, wato ranar 9 ga watan Day a cikin kalandar Iraniyawa a wannan shekara ranar ta fada kan 29 ga watan Decemba.

Fatan da kasashen yamma da kawayensu suke so, na harban tsutsaye biyu da jifa guda bai kai labari ba.

Suna son sus a mutanen Iran su debe kauna daga hukumar zaben kasar, su nuna masu cewa babu adalci a cikin ayyukanta, sannan daga nan su nuna masu tsarin siyasa na musulunci bai dace da wannan zamanin ba. Duk sun tashi a iska.

A lokacin wadannan tashe tashen hankula dai hukumar zabe ta kasar Iran ta kira dukkan yan takaran shugaban  kasa wadanda suke da korafi kan ingancin zaben da ta gudanar, su zo su bayyana inda korafinsu da kuma inda suke ganin an yi masu magudi sai su sake irgen ku’riun a mazabun. Amma wadannan yan Takara biyu wadanda suka tara mutane don cimma manufofinsu, da kuma sharewa kasashen yamma hanya don wargaza JMI sun ki zuwa. Su dai sun dage kan cewa, sai dai a sake zaben.

Har’ila yau shugaban Amurka na lokacin Barak Obama da sauran shuwagabannin kasashen yamma sun fito fili sun bayyana jin dadinsu da abinda yake faruwa a kasar Iran. Sun kuma bayyana cewa suna goyon bayan masu zanga-zanga wadanda suke wargaza kasarsu da kansu, kuma suna jiran Randa zasu ji cewa tsarin musulunci wanda aka kafa a shekara 1979 a kasar Iran ta rushe.

Kasashen yamma sun so su amfani da tsarin ‘juyin juya halin kaloli’ wanda suka yi amfani da shi a kasar Ukrain a shekara 1914 suka kada gwamnati wacce take kusa da kasar Rasha suka kuma kawo Volodimir Zelesli mai biyayya ga bukatunsu a gabacin turai kan kujerar shugabancin kasar a lokacin.

Daon haka ne masu zanga-zanga a bayan zaben shugaban kasa a Iran a shekara ta 2009 suka zabi launin kore. Wato suna son su yi juyin juya halin mai launin kore a kasar Iran.

Amma ga shi yau shekaru 15 kenan ta zanga-zangar goyon bayan JMI bayan tashe-tashen hankula da aka yi lokacin ya wace, amma JMI tana nan daram kan kafufuwanta tana kuma kara karfi.

Sai dai zamu gane irin muhimmancin da kasashen yamma musamman Amurka suka sanyawa rikicin zabe a kasar Iran a shekara ta 2009 ne idan mun koma baya mun ga irin kokarinda suka yi na kawo karshen JMI tun tana jaririyarta har ta kai matsayin da ta kai a halin yanzu.

Da farko a lokacinda Imam Khomaini (q) ya kwace iko da kasar Iran a ranar 11 ga watan Fabrayrun shekara 1979, ya kifar da gwamnatin sarakuna wadanda suke mulkin Iran tun fiye da shekaru 2500 da suka gabata, wato tsarin sarauta ne yake mulkin Iran tun kafin addinin musulunci ya shigo kasar. Kuma bayan haka sarakuna ne suke iko da kasar da sunan addinin musulunci. Har zuwa dangin Pahlawi wadanda Juyin juya halin musulunci ya kauda su, sannan aka kuma kawo tsarin addinin musulunci a kasar.

A lokacinda hakan ya faru Amurka fiye da 70,000 suke rayuwa a cikin kasar Iran mafi yawansu a birnin Tehran, a matsayin masu bawa sarki sha shawara a kan al-amura da dama wadanda suka hada da tsaro tattalin arziki da sauransu. Don haka bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci sun bar kasar.

Amma suna tare da wakilansu a cikin sojoji da kuma jami’an tsaron da suka yi aiki da su, wadanda suke cikin kasar.

Shugaban kasar Amurka na lokacin, Jimmy Carter ya shirya juyin Mulkiwa jaririyar JMI a lokacin amma aka gano Shirin tun kafin juyin mulkin ya kankama, sannan bayan da daliban jami’an Tehran suka kama jami’an ofishin jakadancin Amurka a nan birnin Tehran su kimani 52 suka tsare, tare da bukatar shugaba Carter ya mika masu sarki sha don a hukunta shi kan laifukan da ya aikata a Iran, Amurka ta yi wani Shirin na shigowar sojojinta na musamman kasar Iran don kwato wadannan jami’an ofishin jakadancin ta da ke hannun gwamnatin Iran na lokacin , Amma shima Shirin ya wargaje a garin tabas take wani yankin Hamada na kasar Iran inda jiragen suka fadi suka kama da wuta.

Daga baya dai wannan ne ya zama musabbabin faduwar jam’iyyar Cater a zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a kasar Amurka a shekarar. Carter ya so ya sake samun shugabancin kasar Amurka karo na biyu, amma wannan rikicin na kasar Iran da ya gagareshi ya sa jam’iyyarsa ta fadi a zaben.

Bayan haka sun ingiza shugaban kasar Iraki na lokacin, ya farma kasar Iran da yaki, da sunan bai kuma yarda da yarjeniyar sulhu da suka kulla da kasar a shekara 1975 kan rabon kan iyaka tsakanin kasashen biyu ba. Don haka ya bayyana cewa a cikin kwanaki uku yana ganin zai sha sha’I a birnin Tehran, ganin sojojin Iran a lokacin sun yi Rauni, sun kama gaji saboda juyin mulkin da aka yi a shekara 1979.

Amma wannan ya kai shekaru 8 suna fafatawa da JMI, kasashen yamma a wancan lokacin suna taimakawa Sadam Hussain ta makamai. Daga ciki har da makaman Guba wadanda kasar Jamus ta bawa Sadam Hussain ya kuma yi amfani da su kan mutanen kasar Iran, da kuma kan kurdawan kasarsa, wadanda a lokacin suke neman kafa kasarsu ta kurdawa.

Banyan yaki na shekaru 8 tsakanin makobtan kasashen biyu, ana kawo karshen yakin a shekara 1988, shekara guda kafin rasuwar Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI.

Kada ku manta a duk tsawon shekaru 8 wanada Iran take yaki da kasar Iraki kasashen yamma sun dorawa JMI takunkuman tattalin arziki na makamai da kasuwanci da sauransu. Kuma a ko wace shekara suna kara yawan takunkuman da suke dorawa kasar.

Takunkuman tattalin arziki mafi munin da kasashen yamma suka dorawa JIM bayan nasarar juyin juya halin musulunci sune wadanda shugaba Donal Trump ya dorawa kasar a shekara 2018. Bayan ya fice daga yarjeniyar nukliya tsakanin Iran da sauran manya manyan kasashen duniya wadanda ake kira 5+1 da Iran.

Amma godiya ta tabbatar ga All..wadannan takunkuman duk tare da cewa sun gurgunta tattalin arzikin kasar Amma kuma sun sa kasar dukufa don samar da mafi yawan abub uwan da kasar da kuma mutanen kasar suke bukata daga cikin gida.

A bangaren makamai dai kasar ta kai matsayin wadata da mafi yawan makaman da take bukata. A bangaren da har yanzun kasar take shan wahala saboda takunkuman dai sun hada da jiragen fasinja, wadanda manya manyan kasashen duniya daga kasashen yamma suka yi babakere a kansu. Kamfanonin Boeng da Airbus ne suke samar da mafi yawan jiragen saman fasinja masu inganci wadanda ake amfani da su a duniya.

Don haka jajircewar   JMI ya sa a cikin wata mai kamawa zata yi bukukuwan cika shekaru 47 da kafuwa. Kuma akwai fatan dukkan wadannan hahalhalun zasu wuce a wani lokaci nan gaba. Inda zamu ce siyar addinin musulunci ya shiga cikin siyasar kasashen duniya har’abada. Musamman bayan gazawar makiya a ranar 9 ga watan Day a shekara ta 1388 HSH ko 29 ga watan Decemban shekara ta 2009.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: juyin juya halin musulunci ranar 9 ga watan Day wadanda suka hada da kasashen yamma sun shekara ta 2009 tattalin arziki birnin Tehran a kasar Iran wadanda suke kawo karshen a shekara ta masu sauraro manya manyan zanga zangar goyon bayan da sauransu

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Iran Ta Mayar Da Martani Ga Shawarar Shugaban Amurka Kan Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira

Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland.

Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa daga tushensu.

Arqchi ya kuma mayar da martani ga tashar ta Sky News kan tambayar ‘yancin da ‘yan sahayoniyya suke da shi na rayuwa, inda ya ce: “Kowane dan Adam na da ‘yancin rayuwa, amma babu wanda ke da hakkin ya mamaye kasar wani, wannan kasa ta Falasdinawa ce, dole ne Falasdinawa su yanke shawara da kansu game da makomar kasarsu”.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugabannin Hamas A Ziyararsa Doha
  • Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
  • MDD: Yaran Gaza 2,500 na fuskantar mutuwa matukar ba a yi  gaggawar kwashe marasa lafiya ba
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Bukatar Bunkasa Alakarta Da Kasar Qatar
  • Jigilar Fasinjoji Da Jiragen Kasa Masu Zirga Zirga Cikin Biranen Sin Suka Yi Ta Karu Da Kaso 9.5 A 2024
  • Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kaddamar Da Shirin Tallafawa Masu Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i
  • Kasar Iran Ta Mayar Da Martani Ga Shawarar Shugaban Amurka Kan Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
  • Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar Shekara