HausaTv:
2025-02-01@08:50:44 GMT

Hizbullah Ta Yi Alhinin Sahadar Muhammad Dhaif Kwamandan Rundunar Kassam Ta Hamas

Published: 1st, February 2025 GMT

A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif  tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da  suka taka a fagen gwagwarmaya.

Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa da kuma al’ummar Falasdinu.

Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta mika sakon ta’aziyyar ga iyalan shahidan.

Kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Lebanon ta kuma ambaci cewa, Muhammad Dhaif ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne wajen fada da ‘yan sahayoniya da kwankwasar kansu, musamman ma dai a yayin farmakin Aksa, da ya kasance daya daga cikin fitattun wadanda su ka shriya shi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Abin Da Ya Sa Masu Ruwa Da Tsaki Suka Gana Da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur

A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai.

Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen man da sauki daga gun matatun main a Dangote da kuma na MRS.

A cewarsa, a yanzu haka ‘ya’yan IPMAN na yin dakon man daga gun wadannan matatun biyu, ba tare da matatun sun yi masu karin farashin man ba, inda ya shawarci sauran ‘ya’yan kungiyar da su je su yi rijista da wadannan matatun, domin su rinka sawo man da sauki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abin Da Ya Sa Masu Ruwa Da Tsaki Suka Gana Da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
  • Gwamnan Kaduna Ya Kare Shirinsa Na Sulhu Da ‘Yan Bindiga
  • Abu Obeida ya sanar da shahadar shugaban Hamas Mohammad Deif
  • Kungiyar Hams Ta Jinjinawa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Goyon Bayan Gwagwarmaya
  • Kungiyar Hamas Ta Lashi Takwabin ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa
  • Gwamnatin Kasar Rwanda Ta Ce Zata Ci Gaba Da Goyon Bayan Kungiyar Yan Tawaye Ta M23 A Congo
  • Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya
  • Wata uku uami’o’i ba su da wutar lantarki —SSANU
  • ‘Yan Tawayen M23 Sun Kara Shimfida Ikonsu A Garin Goma