Limamin Juma’ar Tehran Ya Jinjinawa Wanda Ya Assasa Juyin Musuluncin A Iran Marigayi Imam Khumaini ( R.A)
Published: 1st, February 2025 GMT
Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin.
Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da falsafa.
Limamin juma’ar na Tehran wanda yake jawabi dangane da zagayowar cikar shekaru 46 daga dawowar Imam Khumaini Iran bayan zaman hijira na shekaru 15 a kasashen waje, ya ce abin alfahari ne yadda wannan rana ta zagayo a daidai wannan lokacin da kungiyoyin gwgagwarmayar musulunci suke kara bunkasa da daukaka a duniyar musulunci.
Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma bayyana cewa abinda yake da muhimmanci a wannan lokacin shi ne ci gaba da aiki akan tafarkin Imam Khumaini cikin tsayuwar daka ba tare da girgiza ba.
Limamin juma’ar na Tehran ya ce kamar yadda abokan gabarmu suke jurewa wajen fuskantarmu, to mu ma ya zama wajibi a gare mu da mu yi tsayin daka wajen fuskantarsu, tare da yin ishara da abinda ya faru a Gaza, da kuma kallafaffen yaki akan Iran yana mai kara da cewa; Ba domin gwagwarmaya ba ta al’ummar Iran da su ka hada da dakarun kare juyin musulunci da sojoji a wancan lokacin, to da abubuwan da suke faruwa na alfahari ga al’ummar Musulmi a wannan lokacin ba su faru ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Kai Hare-hare Akan Birane Mabanbanta Na Kasar Yemen
Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda yake gabashin birnin San’aa.
Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka din sun kai hare-haren ne a tsakanin marecen jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis.
Daga cikin wuraren da aka kai wa harin jiya da marecen da akwai Sahlin dake karamar hukumar Ali-Salim. Sau 6 Amurkan ta kai wa yankin hare-hare.
Da safiyar yau Alhamis kuwa jiragen yakin na Amurka sun kai hare-hare a gundumar Sa’adah.
Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren su ne, al-tahita, dake kudancin gundumar Haudaidah, a yammacin kasar ta Yemen.
Amurka tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda bayar da kariya ga HKI, da zummar hana Yemen kai hare-hare akan manufofin ‘yan sahayoniya a ruwan tekun ” Red Sea”.
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ba za ta taba daina kai wa HKI hare-haren ba har sai idan an daina kai wa Gaza hari. Bugu da kari ta sanar da cewa;za ta ci gaba da hana jiragen ruwa wucewa ta tekun “Red Sea” har zuwa lokacin da za a kawo karshen hana shigar da kayan agaji cikin yankin na Gaza.