Fizishkiyan: Gwagwarmaya Za Ta Yi Karfin Da Ba Za Iya Rusa Ta Da Makamai Ba
Published: 1st, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga.
Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna.
Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe mai girma na matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta a wannan lokacin sakamako ne na nesantar koyarwar al’kur’ani, wanda kuma babu abinda hakan yake haifarwa sai rabuwar kawuna da kuma bude kafa a gaban makiya ‘yan adamtaka.”
Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce; shi alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da dukkanin bil’adama ba tare da la’akari da launinsu ko ajinsu ba, ko kuma addinin da suke yi,kuma ya nuna wa jinsin dan’adam hanyar kai wa ga kamala.
Haka nan kuma shugaban na kasar Iran ya ce, a karkashin koyarwar addinin musulunci, mutane za su sami madogara mai karfi mai nagarta a cikin wannan duniyar da take cike da rudani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Ta Bayyana Matsayinta A Shirin Makamashin Nukliya Na Kasar
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, mai yuwa yayi tasiri a barazanar da kasar Iran take fuskanta na kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar.
Aragchi ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran na zaman lafiya ne, kuma har yanzun kasar Iran tana kan bakanta na aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya don kare hakkinta na mallakar fasahar makamashin nukliya wannan dokokin kasa da kasa duka bada.
Ministan ya bukaci hukumar , a irin wannan halin da Iran take ciki na fuskantar barazana ga cibiyoyinta na makamashin nukliya, akwai bukatar kwarai da gaske ga hukumar ta IAEA ta fito fili ta bayyana matsayinta.
A nashi bangaren babban daraktan hukumar makamashin nukliya ta duniya, Rafael Gorossy ya ce a shirye yake ya shiga tsakanin bangarorin biyu don tattaunawa da kuma fahintar juna kan wannan matsalar.