HausaTv:
2025-04-02@15:57:03 GMT

DRC: ‘Yan Tawayen M 23 Sun Sha Alwashin Tunkarar Babban Birnin Kasar Kinshasha

Published: 1st, February 2025 GMT

Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga  babban birnin kasar Kinsasha.

Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu  ita ce, muna yin yaki ne saboda kishin Congo, ba muna yaki ne saboda samun ma’adanai ba, babu wani dalili na daban da ya sa muke yaki.

Da akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa, ‘yan tawayen na M 23 sun kama hanyar zuwa Bukavu, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a yankin.

Nangaa ya ce babu wata gwamnati tsayayya a kasar Congo, domin Tshikedi ya riga ya rusa sojoji, ‘yansanda, kuma tsarin tafiyar da mulki, haka nan kuma ma’aikatar shari’a.”

Sai dai kuma ‘yan  tawayen sun ce a shriye suke a bude tattaunawa domin a dama da su a cikin sha’anin tafiyar da kasar.

Kungiyoyin kasa da kasa suna yin kira da a tsagaita wutar yaki a kasar ta DRC.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Yakin Neman Zabe A Kasar Gabon

Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan daga baya ya sauka don ya sake dawowa da hanyar zabensa ya fara yakin neman zabe a jiya, inda yake kira ga mutanen kasar su zabe shi saboda kyautatuwar kasar Gabon.

A cikin watan Augustan shekara ta 2023 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya gaji babansa Umar Bongo bayan rasuwarsa ba tare da zabe ba.

A halin yanzu dai yan takara 8 ne suke neman wannan kujerar a zaben ranar 12 ga watan Afrilu. Idan ba’a sami wanda ya lashe zaben ba za’a sake gudanar da zabe tsakanin wadanda suka zo na daya da kuma na biyu a zagayen farko.

Shugaban kasa a Gaban, yana yin shugabnci na tsawon shekaru 7 a zagaye na farko idan ya sake tsayawa ya kuma ci zabe yayi zagaye na 2 wanda zai kaishi ga shekari 14 na shugabaci. Daga nan shi ba zai tsaya ba, kuma wani daga cikin danginsa ba zai tsaya ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka
  • Kasar Sin Mai Tabbatar Da Daidaito A Duniya Mai Cike Da Rashin Tabbas
  • Kungiyar “Amnesty” Na Zargi Netanyahu Da Aikata Laifukan Yaki
  • Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
  • Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka
  • Gwamnati Za Ta Inganta Wuraren Tarihi Domin Nishadantarwa A Duk Jihohin Nijeriya 
  • An Fara Yakin Neman Zabe A Kasar Gabon
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Sabbin Hare-Hare Kan Kasar Yemen A Daren Jiya
  • Girgizar Kasa: Shugaban Kasar Myanmar Ya Mika Godiya Ga Tawagar Likitocin Yunnan Ta Kasar Sin
  • An Hori Dagatan Kasar Zazzau Su Sa Ido Akan Bakin Fuskokin A Yankunan Su