HausaTv:
2025-03-03@16:58:14 GMT

An Sake Wani Sabon Hatsarin Jirgin Sama A Amurka

Published: 1st, February 2025 GMT

Kafafen watsa labarun Amurka sun sanar da cewa wani karamin jirgin sama ya fadi akan wata cibiyar kasuwancin dake Philadelphia  a jihar Pennsylvania tare da kashe mutane 6 da suke cikinsa.

Kafafen watsa labarun na Amurka sun ce ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar da ta tashi a cikin gidaje da dama a yankin da jirgin ya fado.

Tashar talabijin din “Fox News” ta sanar da cewa jirgin da ya fado na jigilar marasa lafiya ne, yana dauke da  wani mara lafiya daya da dan’uwansa, sai kuma likitoci biyu da suke tare da shi.

Ita kuwa jaridar “Philadelphia Enquiry” ta ambato ‘yan sanda suna cewa, jirgin ya fado ne da misalin karfe 6;pm agogon yammacin gabashin Amurka.

A ranar Larabar da ta gabata ma an sami hatsarin jirgin sama na matafiya wanda ya ci karo da wani jirgin soja mai saukar angulu da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 67, wanda ake dauka a matsayin daya daga cikin mafi munin hatsarin jiragen sama da aka yi a Amurka a cikin shekaru 25.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas: Babu Wani Karin Tattaunawa Da HKI, A Aiwatar Da Yarjeniyar Kamar Yadda Take

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘ba zamu tsawaita kashi na farko na yarjeniyar ba, haka ma ba za mu amince da gabatar da sauye –sauye a cikin yarjeniyar ba. Mardawi yace HKI za ta karbi fursinonin da suka rage a hannun Hamas kadai ne, ta hanyar ko tsarin da yarjeniyar ta amince da shi. Ya ce: Benyamin Natanyahu yana, cikin dimwa idan ya na son amfani da yunwa a matsayin makami don samun abinda ya kasa samu da makamai ba. HKI ta bada sanarwan cewa za ta dakatar da dabbaka yarjeniyar sulhu da Hamas bayan an kammala kashi na farko na Yarjeniyar, kuma zai dakatar da shigar abinci yankin Gaza idan an kammala kashi na farko na yarjeniya.

Kafin haka Netanyahu ya ce ya amince da shawarar da jakadan shugaban kasar Amurka Donal Trump, Steve Witkoff ya gabatar na tsawaita bangare na farko a yarjeniyar saboda watan Ramadan.

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Wassem ya ce: kungiyar tana tuntubar masu shiga tsakani a aiwatar da yarjeniyar , a kai a kai, don ganin al-amura sun koma kamar yadda yakamata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Miji ya amince saurayin matarsa ya tare a gidansu
  • Hamas: Babu Wani Karin Tattaunawa Da HKI, A Aiwatar Da Yarjeniyar Kamar Yadda Take
  • Masana Fasahar Gina Jiragen Sama A Iran Sun Samar Da Wata Fasahar Nano Mai Rage Nauyin Jiragen Sama
  • Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza
  • Ramadan: Hon Jaji Ya Ƙaddamar Da Tallafin Abinci Ga Mutane Sama Da 500,000 A Zamfara
  • Hamas: Matakin Netanyahu na hana shigar kayan agaji a Gaza keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne
  • Masar ta ki amincewa da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • An kama ɓarayin waya a Kano
  • Gobara ta ƙone sashen wani asibiti a Legas