Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara
Published: 1st, February 2025 GMT
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa.
A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa.
Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya.
Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya.
Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a ZamfaraKhalifa Mahi Inyass ya shaida wa manema labarai cewa tawagar ta taso ne musamman daga ƙasar Senegal, mahaifar Sheikh Ibrahim Inyass, domin halartar Maulidin Tijjaniyya na Sheikh Inyass na wannan shekara.
Ya ba wa Shugaba Tinubu tabbacin goyon baya da addu’o’i musamman daga mabiya ɗarikar Tijjaniyya sam da miliyan 400 da ke Najeriya da sauran wurare.
’Yan tawagar sun haɗa da Sheikh Ibrahim, babban ɗan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da dai sauran shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Darikar Tijjaniyya Inyass Mahi Ibrahim Inyass Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Saliyo Julius Maada Bio a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ganawar tsakanin shugabannin ƙasashen Afirka biyu ta gudana ne a bayan labule, inda jami’an gwamnati kalilan ne suka halarta.
NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu ruwa da tsaki kan illar bautar da yaraShugaba Bio ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 12:30 na rana, kuma ya samu tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.
Haka kuma, shugaban na Saliyo ya samu tarba ta ban girma, inda rundunar sojojin shugaban ƙasa suka yi masa fareti tare da kade-kaden gargajiya.
Duk da cewa ba a san ajandar wannan ganawa ba, sai dai Aminiya ta samu cewa ba zai rasa nasaba yunƙurin inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu ba.
Nijeriya da Saliyo mambobi ne na ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka da kuma ƙungiyar tarayyar Afrika, kuma sun haɗa kai kan tsare-tsaren da suka shafi samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a yankin.
Nijeriya ta taka rawar gani wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashen Afirka da dama musamman Saliyo.