Abubuwa Biyar Da Ya Kyautu A Mayar Da Hankali A Kansu A Kakar Noman 2025
Published: 1st, February 2025 GMT
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024.
1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024.
Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024.
Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma magance yunwa.
Sai dai wasu manoman sun ce, rashin tsaron ya ragu a wasu Jihohin Arewacin Kasar da lamarin ya fi yin kamari.
2. Sauyin Yanayi: Wannan lamari ya zama tamkar ruwan dare a fadin duniya, wanda kuma yake jawo sauya tsarin noma, misali a 2024, wasu manoma a sassan Arewacin Nijeriya, sun koka kan rashin samun saukar ruwan sama a kan lokaci, wanda hakan ya jawo ba su samu wani yin girbi mai kyau ba.
Masana sun yi hasashen cewa, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, sauyin yanayi zai zama babbar barazana a kakar noma ta 2025, wanda kuma rashin daukar matakan kan iya haifar da hauhawar farashin kayan abinci.
A cewar wani rahoto na Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Duniya (FAO), ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma afkuwar annobar ambaliyar ruwan sama a 2024, ya lalata sama da tan miliyan daya na amfanin gona, wanda wannan adadi zai iya ciyar da mutane miliyan 13.
Kazalika, a watan Satumbar 2024, Dam din Alau Dam ya jawo mummunar ambaliyar ruwa, inda ya lalata hakta kimanin 700,000 a cikin kimanin gonaki 200.
Har ila yau, a 2024; sauyin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwan sama a Jihohin Borno, Bauchi, Sakkwato da kuma Jigawa.
3- Barkewar Cututtuka A Gonakin Da Kwari Suka Lalata Amfanin Gona: Misali cutar da lalata Citta da cutar murar tsintsaye da kuma cutar da ke lalata tumatir a 2024, sun yi matukar barna.
Akwai cutar da ta lalata wasu gonaki na Citta, wanda adadin kudin suka kai kimanin Naira biliyan 12 a 2023.
Manoma sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi a dauki matakan gaggawa tare da samar da dauki, domin dakile wadannan cututtuka a 2025.
4- Tsadar Farashin Kayan Gudanar Da Aikin Noma: Manoma sun fuskanci hauhawar farashin kayan da ake gudanar da aikin noma.
Wata kididdiga ta nuna cewa, farashin Man Fetur na haifar da hauhawar farashin kayan abinci, sannan kuma manoma da ‘yan kasuwa sun koka kan haramtaccen harajin na ‘yan na kama ke kakaba musu, bayan sun yo jigilar amfanin gona.
5- Hauhawar Farashin Kayan Noma: Tsadar farashin takin zamani, injinan ban ruwa, tsadar Irin noma, sun kasance manyan kalubale ga manoma, wanda hakan kuma ke shafar girbin amfanin gona.
Saboda tsadar ingantaccen Irin noma, hakan ya tilasta wa manoma sayen Iri, wanda ba shi da wani inganci.
Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi a 2025, a kawo karshen wannna matsalar, domin samar da wadataccen abinci a kasar.
কীওয়ার্ড: sun bayar da
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Jaddada Ciyar Da Shirin Kasar Sin Mai Kwanciyar Hankali Zuwa Babban Mataki
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp