Jiragen Saman Yaki Na JMI Suna Amfaniya Da Kayakin Zamani A Aiyukan Sojen Da Suke Yi A Kasar
Published: 1st, February 2025 GMT
Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne.
Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda zasu nunasu nan ba da dadewa ba.
Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda ya nakalto babban kwamnadan sojojin sama na JMI Bugedia Janara Hamid wahidi yana fadar haka.
Wahidi ya kammala da cewa sojojin sama na JMI a shirye yake su aiwatar da umurnin babban kwaman dukkan sojojin kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Zai Kori Dabilai ‘Yan Kasashen Waje Da Suke Goyon Bayan Hamas Daga Amurka
Wani jami’in fadar mulkin Amurka ( White Hosue) ya nakalto shugaban kasar Amurka Donald Trump yana fada a yau Laraba cewa, shugaban kasar Amurkan ya rattaba hannu akan wata doka ta fada da kin jinin yahudawa da ta kunshi cewa duk wasu dalibai ‘yan kasashen waje da masu ci rani a kasar, idan su ka shiga cikin Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa to za a kore su daga Amurka.
Dokar da Trump din yta sanya hannu a kanta ta kuma kunshi bayar da umarni da ma’aikatar shari’ar kasar aka cewa ta bi diddigin duk masu barazanar ta’addanci, da ruruta wutarsa, da mabarnata dake cutar da yahduawan Amurka.”
Haka nan Trump ya ce zai soke izinin shiga cikin kasar ta Amurka da aka bai wa dalibai masu goyon bayan Hamas a cikin dukkanin jami’o’in kasar.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya aikewa da dukkanin cibiyoyin kasar ta Amurka umarnin su dauki matakan da su ka dace domin fara korar duk masu fada da Yahudawa, daga ciki har da dabilan jami’oi.
A tsawon lokacin yakin da HKI ta shelanta akan al’ummar Falasdinu, daliban jami’o’in kasar ta Amurka sun rika yin Zanga-zanga da gangami na nuna kin amincewa da halayyar ta Isra’ila, da kuma yin kira ga gwamnatin Amurka da ta kawo karshen sayar da makaman da take yi mata.