Shugaban Kasa Da Ministocinsa Sun Jaddada Bai’a Ga Wanda Ya Kafa JMI A Safiyar Yau Asabar A nan Iran
Published: 1st, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran, shekaru 46 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Asabar ce shugaban kasar Iran, Masuod Pezeshikyan tare da majalisar ministocinsa suka kara sabonta bai’a wato marigayi Immam Khomani (q).
Labarin ya kara da cewa Sayyid Hassan Khomani, jikan Imam(q) wanda kuma yake kula da hubbaren nasa ne, ya tarbi shugaban kasar ya kuma jagorance su zuwa hubbaren kakansa Imam Khumaini(q).
Imam Khomani (q) ne ya jagoranci mutanen kasar Iran zuwa kifar da gwamnatin sarki sha, shekaru 46 da suka gabata, a ranar 11 ga watan Fabrayrun shekara ta 1979.
Wannan dai yana daga cikin Jerin shirye-shiyen da aka tsara na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran. Wanda za’a kamala shi a ranar 22 ga watan Bahman na shekara ta 1403.
Ana fara bukukuwan cika shekaru 46 da nasarrar juyin juya halin musulunci a kasar Iran ne tun ranar 1 ga watan Farairu 2025 a duk fadin kasar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: shekaru 46 da
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin.
Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe akalla Falasdinawa 80 a ranar Lahadi.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kai mutane 53 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci a Gaza a ranar Lahadin, wato ranar farko ta bikin Eid al-Fitr.
Ma’aikatar ta kara da cewa, “har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine, saboda masu ceto ba su iya kai musu dauki.
A ranar 18 ga Maris, ne Isra’ila ta sake dawo da kai farmaki Gaza wanda ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da ta fara aiki a watan Janairu.
Ana kuma tuhumar Isra’ila da laifin kisan kiyashi a gaban kotun kasa da kasa saboda yakin da ta yi da yankin.