Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Matakan Da Amurka Zata Bi Don Kyautata Dangantaka Da Iran
Published: 1st, February 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin Doga.
Ministan ya kara da cewa gwamnatocin Amurka da suka shude daga ciki har da gwamnatin Trumps suka yi a baya musamman ficewarta su daga yarjeniyar JCPOA.
Abbas Argchi ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci wanda dole ne Amurka ta yi idan tana son jawo hankalin iran dangane da tattaunawa da ita shi ne sako kudaden ta masu yawa wadanda ta hana a yi amfani da su a wurare da dama a duniya.
Ministan ya ce wannan yana iya zama mataki na faro wanda gwamnatin Amurka zata iya dauka idan tana son haka.
Kafin haka dai gwamnatin sabuwar gwamnatin Amurka tana ganin tattaunawa da kasar Iran ita, tana ganin hanyar da zata da ita, don warware matsaloli daban-daban da suke tsakaninsu. A wannan karon.
Sannan ya kara da cewa idan har tana son al-amura su tafi mata yadda take so, ya kasance tattaunawar ta shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya ce kadai za’a yi magana a kansa, kada ta hana da wasu al-amura, musamman rawar da irin take takawa a yankin Asiya ta kudu.
Kafin haka dai gwamnatin Donal Trumps a zagayen na farko ne ta fidda Amurka daga yarjeniyar JCPOA wacce aka kulla da gwamnatin Obama a shekara ta 2015, kuma ta fice daga cikinta a shekara ta 2018 sannan ta sake dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kar wadanda suke aiki har yanzun.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lavrov Ya Yi Watsi Da Batun Aike Wa Da Dakarun Zaman Lafiya A Kasar Ukiraniya
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai.
Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a ci gaba da yaki.
Sergey Lavro ya kuma ce; tunanin aikewa da dakarun zaman lafiya zuwa Ukiraniya wauta ce.
Lavrov ya bayyana shugaban kasar Ukiraniya Zelenskiyda cewa dan Nazi ne, wanda ya ha’inci al’ummarsa.”