Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu
Published: 1st, February 2025 GMT
Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta.
Daga watan Disamban 2024 da Hisbah ta yi sanarwar zuwa yanzu, an samu ɓullar aƙalla bidiyoyi 10 daga jihar da suka tayar da kura a kafofin sada zumunta, musamman TikTok, ciki har da na tsiraici.
Ɓullar bidiyon tsiraicin fitattun ’yan Tiktok irin su Hafsat Babaiana da Hafsat Fagge ne, dai suka fara gyaran hanya ga sauran ’yan soshiyal midiya musamman TikTok.
Hakazalika an ga wasu ’yan Tiktok da suka yi ƙaurin suna wajen yaɗa irin waɗannan bidiyoyin suka tsere daga Kano a lokacin da Hisbah ke kamen suna ta dawowa.
Kano ta zama matattarar ’yan TikTokLamarin ya kai ga ana iya cewa Kano ta koma matattarar ’yan TikTok, inda ake ganin irin bidiyoyin da suke yi sai ƙara muni suke yi.
Ko a kwanakin baya hukumomin jihar sun gargaɗi ’yan TikTok da suka ɓullo da salon tsayar da ababen hawa su yi bidiyon barkwanci a tsakiyar titi, cewa su shiga taitayinsu.
A halin yanzu baƙi har daga ƙasashen waje zuwa suke Kano, inda kowannensu ke sheƙe ayarsa a Kano.
Daga cikin waɗanda a baya suka tattara komatsansu daga jihar amma yanzu suka dawo akwai ɗan daudun nan Hassan Makeup ɗan asalin Jamhuriyar Nijar, wanda ake ganin munin bidiyoyin da yake yi a yanzu ya dama na da sun shanye.
Yadda ’Yan TikTok a Kano ke yamutsa hazoA cikin baƙin ’yan ƙasa da suka dawo jihar suke tayar da ƙura akwai irin su Rahama Sa’idu, wadda ta fara tashe a kafofin sada zumunta bayan da aka kore ta saboda rashin cin jarabawar ƙarshe daga Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Jihar Kebbi.
A kwanakin bayan Rahama ta sake yamutsa hazo, inda makonni kaɗan da korar ta daga makarantar, ta fito Tiktok tana nuna sabuwar motarta ƙirar Mercedes Benz GLK da sabuwar wayar iPhone 16.
Lamarin da ya sanya masu bibiyar ta ɗora mata alamar tambaya kan haƙiƙanin yadda ta same su ba tare da tana wata sana’a ba.
Bayan kwanaki Rahama ta buɗe katafaren shagonta na sayar da kayayyaki a Kano, wanda shi ma ya sa wasu nuna damuwa kan inda ta ke samun tarin dukiyar a lokaci ƙanƙani.
A baya-bayan nan kuma akwai dambarwar auren G-Fresh Al’amin da Alpha Charles Borno, inda suka dinga yin bidiyon runguma da sumbatar juna, wanda shi ma ya saɓa wa al’ada da Musulunci, addinin G-Fresh ɗin.
Kwanaki kaɗan bayan batun auren nasu ya yamutsa hazo kuma suka sanar cewa sun fasa auren juna.
Hakazalika akwai sauran fitattun ’yan Tiktok irin su Hadiza Mai Bakin Kiss da Mai Wushirya da Babiana Queen of Update, da ake ganin suna cin karensu babu babbaka a jihar ta hanyar yaɗa makamantan waɗancan bidiyoyin.
Operation Kau da BadalaA shekarar 2023 ne Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ƙaddamar da shirin samame da ta yi wa take da “Operation Kauda Baɗala”, inda ta riƙa bi otel-otel da wuraren shaƙatawa tan kamo masu aikata baɗala.
A samamen farko ne Hukumar ta kamo samari da ’yan mata a sassa daban-daban na jihar, cikinsu har da ɗaliban manyan makarantu ’yan ciki da wajen jihar, ta jibge su a ofishinta, domin gudanar da bincike.
Kamen, ya janyo wa hukumar kakkausar suka kan yadda jami’anta suka dinga cicciɓar matan da suka kama a wuraren suna cusa su a mota.
A ɗaya ɓangaren kuma sun samu yabo musamman kan gayyatar iyayen ɗaliban domin yi musu wa’azi da jan hankalinsu kan abubuwan da ’ya’yansu ke aikatawa a bayan idonsu.
Tsaftace soshiyal midiyaDaga nan ne hukumar ta juya kan masu harkar nishadi, musamman ’yan Tiktok da Facebook da ’yan fim, inda ta yi zama a lokuta daban-daban da su da nufin lalubo hanyar tsaftace harkokinsu da kuma samar musu da shugabanci, domin jin kokensu.
Fitattaun ’yan Kannywood da TikTok irin su Murja Kunya da Hafsat Babiana da Abdallah Amdaz da Shugaban Hukumar Tace fina-fianai ta Jihar Kano, Abba Al-Mustapha, sun halarci zaman, inda suka bayar da shawarwari kan mafitar da suke ganin ta dace a ɗauka domin yaƙi da baɗalar.
A yayin zaman ne ’yan TikTok da takwarorin nasu suka yi alƙawarin daina yaɗa bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci a jihar.
To sai dai kwanaki kaɗan bayan nan ne ’yan Tiktok irin su Murja Kunya da Hafsat Fagge da Hafsat Babiana da G-Fresh Al’amin suka yi tuban muzuru inda aka koma yin irin bidiyoyin da suka yi alƙawarin dainawa.
Dambarwar Murja KunyaA shekarar 2024 ne al’ummar unguwar da Murja ta ke suka kai ta ƙarar ta ga Hisbah, cewa matashiyar tana neman ɓata musu tarbiyyar ’ya’ya saboda yanayin shigarta da abubuwan da ta ke aikatawa a layi a kan idon jama’a.
A ƙarshe hukumar ta kamo Murja ta gurfanar da ita a kotu, har alƙalin ya bayar da umarnin tsare matashiyar a gidan yari.
Wani abin da ya ɗauki hankali a dambarwar Murja, shi ne yadda ta yi layar zana daga gidan yarin ba da sanin kotu ba, wanda daga bisani jami’an gwamnati suka sanar da cewa su ne suka ɗauke ta domin kare ta.
Daga bisani aka ci gaba da shari’ar kotu ta bayar da belin matashiyar.
A ranar 4 ga watan Fabrairun 2024 ne, Kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a yayin hirarsa da Sashen Hausa na BBC, ya ce hukumar tana tattaunawa da shugabannin Kamfanin Tiktok kan yadda manhajar za ta hana bidiyoyin da suka saɓa da tarbiyyar Musulunci a jihar.
Ya ƙara da cewa suna kuma tattaunawa da majalisar dokoki kan yiwuwar yin dokokin da za su taimaka wajen ɗabbaka tsari da suke tattaunawa da Tiktok.
Gwamna ya kwance wa Hisbah zani a kasuwaSati uku bayan tattaunawar ne, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da yadda Hisbah ke tafiyar da aikin Operation Kau da Baɗala.
Kalaman nasa sun fusata Sheikh Daurawa, inda a anar 1 ga watan Maris ɗin 2024, ya ajiye aikinsa.
Kalaman Gwamnan sun haifar da ce-ce-ku-ce inda wasu ke bayyana cewa hakan ya nuna ya ɗaure wa ’yan soshiyal midiya gindi, ya sare wa Hisbah gwiwa ta koma kyanwar Lami.
Magoya bayansa na ganin jami’an Hisbah sun yi kuskure kuma ba laifi ba ne don gwamna ya gyara musu a matsayinsa na shugaban jihar, amma wasu na ganin kamata kaman tozarta hukumar ya yi, ya daɗaɗa wa masu aikata baɗala.
Duk da cewa daga baya an sasanta tsakanin ɓangarorin bayan ƙungiyar malaman jihar ta shiga tsakanin ɓangarorin tare da tabbacin gwamnati na mara wa Hisbah baya, ana iya cewa tun daga lokacin Operation Kau da Baɗala ya kwanta dama a Kano.
Hisbah ta zama magen lami?Fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Facebook, Dakta Muhsin Ibrahim, wanda ke sukar kamen, ya koka da cewa dainawar ba alheri ba ne ga Kano.
Ya ce, “Dainawa kwata-kwata ba shi ne mafita ba. ɗan adam ajizi ne. Wannan salon kamen bai taƙaita ga Hisbah ba, domin ko a wuraren irin su Berlin da Baltimore da Landan, wani lokacin ana samun jami’an da ke yi wa mutane diɓar karan mahaukaciya lokacin da suke kama su.
“Amma dakatar da kamen gaba ɗaya zai sanya mutane su samu saken yin abin da suka ga dama a Kano.
“Daga lokacin da Hisbah ta fitar da sanarwar daina kamen, wasu da ke wasu jihohin ma da wata ƙasar har sun tattaro kayansu sun dawo sun fara yaɗa bidiyoyinsu yadda suke so a sosiyal midiya.”
Ya ƙara da cewa: “Tabbas Kano gari ne mai ɗauke da mutane iri-iri, amma yana da nasa tarbiyya da al’ada da addinin da ya kamata a ce ana girmamawa.
“Tabbas lokaci ya canja ana samun cakudewar al’adu, amma kuma bai kamata mu bari a b’ɓata mana namu al’adunmu ba. Kowacce ƙasa a duniya na ƙoƙarin kare martabarta ta hanyoyi daban-daban.
“Misali, Muhammad ne sunan da ya fi kowanne farin jini da ake sanya wa jarirai a Ingila da Wales a yanzu, amma hakan ba ya nufin Musulmi a ƙasar na da damar auren mace da fiye da ɗaya.
“Gwamnatin Kano ta sake duba tsarin gudanarwar Hisba, ko dai akwai Hisbar da ke aiki, ko kuma babu. Amma bai kamata ta zama kyanwar Lami ba. Malamai da dama na wa’azi, ba aikin Hisbah ba ne wannan. Allah Ya shiryar da mu. Amin”, in ji shi.
Ya kamata a tauna tsakuwa… – MalamaiFitaccen Malami a Kano, Malam Ali ɗan Abba ya ce duk da cewa wa’azi abu ne mai kyau, amma ya kamata a matsayin Hisbah na Hukuma tana tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro, musamman domin kakkaɓe masu bata wa jihar suna.
“Tun kafin zuwan waɗannan shafukan wasunsu dama kangararru ne. Sai dai fatan addu’a da shiriya da daukar matakan ladabtarwa a kansu.”
Ya ci gaba da cewa, “A wata mahangar masu hange ma, yadda al’adar Kano take da kunya da mutunci da rikkon addini, baki ne suke shigowa su gurbata ta. Saboda zai yi whala a ce an samu gida na gargajiyar Kano da abubuwa na tabara da rashin kirki.”
Abin da ya kamataSai da ya bayyana wadansu matakai da yake ganin ya dace mazauna garin su fara dauka, matukar suna so jihar ta koma matsayinta na cibiyar Musulunci a Arewa.
Ya ce, “A tsari na addinin Musulunci ba a zuba ido idan ana yada barna. Kamar yadda Allah Ya fada, ba ya umarini da aikata alfasha. Don haka duk abin da ya danganci fasikanci da fajirci da sauran irin wadannan abubuwan na rashin albarka da rashin kirki, Annabi (S.A.W) ya bai wa duk wanda yake da dama ikon kau da alfasha da matakai guda uku.Ya ce duk wanda a cikinku ya ga abin ki, to ya canja shi da hannunsa. Idan bai samu dama ba da harshensa, idan ba zai iya ba ya yi da zuciyarsa, wato ya kyamace shi.
“Amma ni jan hankalin da nake da shi shi ne; na farko dole ne kamar yadda Allah Ya danka amanar ’ya’ya a hannun iyayensu, su kula da ita. Mutane su ji tsoron Allah su sani Allah Zai tambaye su. Idan ka so naka duniya za ta ki shi, idan ka ki shi kuma ta so shi.
“Abu na biyu kuma Hisba ta kara kaimi. Ana kokari amma a dada karawa. Salon wa’azantarwar daidai ne. Amma duk wanda bai ji ba ya kamata a ce a yi abin da ake ganin daidai ne domin makaho bai san ana ganin sa ba sai an taba shi. Hukuma ta dinga daukar matakan da suka dace.
“Sannan yana da kyau sauran al’umma kamar kafafen yada labari su dage wajen yada tunatarwa domin wanke zukatan al’umma. Wannan ba zai kawar da badala ba, amma zai rage. Annabi (SAW) ya zo ya koma ga Mahaliccinsa ya bar kafirai da masu yada badala ba a daina ba, don haka ba zai yiwu a daina duka ba.
“Amma a ci gaba da yakar ta. Idan bako ya gurbata dan unguwa dan unguwa zai iya bata unguwa daga nan ya yadu a gari.
Dalilin da muka daina kame — HisbaAminiya ta tuntubi Hukumar ta Hisba kan koken da al’ummar ke yi kan yadda ’yan Tiktok din ke cin karensu babu babbaka a jihar, da kuma matakin da hukumar ta dauka na daina kame.
Hukumar ta bakin Mataimakin Babban Kwamandan Hisba Mai kula da Ayyukan Yau da Kullum Dokta Mujahid Aminudeen Abubakar ta ce ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, kuma nan gaba kadan za ta bayyana matsayarta kan yiwuwar ci gaba da kamen.
“Ganowa muka yi wasu abubuwan da suke janyowa ake ta wannan badalar talauci ne, wasu kuma jahilci ne, wasu rashin sana’a ne. To shi kuma Musulunci cizawa ake yi ana busawa. Kullum ba za ka dauko hanya daya ka ce ita za ka yi ta bi ba, ana so a yaukaka shi, a canja shi, a gyara shi, sannan a kara masa sabon salo.
“Don haka ja da baya ga rago ba tsoron fada ba ne, dabara ce ta yaki. Shi ya sa idan muka fito da wannan salon, sai mu canja mu koma wannan. Idan wannan salon bai yi aiki ba, sai mu sake komawa wani salon. Yanzu muna ta nazari muna so mu gano wanne ne ya fi. Da izinin Ubangiji idan mun gano wannan operation din shi ya fi komai, kwanan nan za a ji mun dawo an ci gaba da kame, an kuma ci gaba da gurfanar da su gaban shari’a.
Inda aka kwana kan tattaunawa da TikTokDangane da batun tattaunawa da kamfanin Tiktok don toshe bidiyoyin da suka saba da dokar hukumar kuma, Dokta Mujahid ya bayyana matakai da suka tsara bi kafin fara aiwatar da shirin.
“Matakan da za mu dauka musamman na soshiyal midiya, matakai ne daban-daban kusan guda biyar. Na farko shi ne mun fara zama da su mu ga yadda za a yi a gyara. Na biyu a kara ilmantar da su. Na uku a ba su sana’ar da ta fi wannan wacce suke yi. Na hudu wadanda suke fitina a samu yadda za ayi a aurar da su. Na biyar shi ne idan duk ya ki yi, shi ne za mu ga yadda za ayi a rurrufe shafukan.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminiya Baɗala Dokta Muhsin Ibrahim Rahoto soshiyal midiya yan TikTok da tattaunawa da yan Tiktok da ya kamata a Ya kamata a
এছাড়াও পড়ুন:
Fannonin Da Xi Jinping Ya Lura Da Su A Ziyararsa A Arewa Maso Gabashin Sin
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara?
Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba.
Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru Kan Naira Biliyan 64Sa’an nan abu na biyu da shugaba Xi Jinping ya sa lura a kai shi ne yadda ake kula da jama’ar da bala’in ambaliyar ruwa ya ritsa da su a bara. Yayin da fanni na uku shi ne yadda kasuwannin wurin suke samar da isasshen kayayyakin abinci masu inganci ga jama’a, a lokacin bikin bazara na gargajiya.
Cikin wata unguwa, shugaba Xi ya ce, wani abu mafi faranta rai shi ne ganin yadda jama’a suke jin dadin rayuwa. Ya ce ya kamata a kara kokarin tabbatar da haka a ko da yaushe. (Bello Wang)