Van Rompuy: Ya Kamata A Kiyaye Cudanya Tsakanin Mabambantan Al’adu
Published: 1st, February 2025 GMT
Wakilin CMG ya yi hira da tsohon shugaban majalisar nahiyar Turai, kuma tsohon firaministan kasar Belgium, Herman Van Rompuy, a kwanan baya, inda tsohon shugaban ya nanata bukatar karfafa cudanya tsakanin al’adun bangarorin yammaci da gabashin duniya.
Herman Rompuy ya ce, ta hanyar cudanya, kowa zai iya koyon sabbin dabarun da yake bukata, kana za a iya tabbatar da fahimtar juna.
Dangane da shawarar raya “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, Mista Rompuy ya ce, ana bukatar tabbatar da saukin jigilar kayayyaki tsakanin kasashe daban daban, gami da ingancin cinikin duniya, ganin yadda suka jibanci wadatar al’ummun kasashen duniya. Saboda haka, yana goyon bayan duk wani matakin da zai amfanawa karfafar hadewar sassan duniya.
Ban da haka, tsohon dan siyasan na nahiyar Turai ya yi tsokaci kan shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dangane da yunkurin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da ingancin cudanyar al’adu a duniya, inda ya ce, shawarwari sun nuna burikan da ake neman cimmawa a kasashe masu sukuni, da wadanda ke kan hanyar tasowa baki daya. Ya ce, dukkan kasar Sin da kasashen Turai za su iya samar da gudunmowa ga yunkurin cimma wadannan manyan burika masu muhimmanci. (Bello Wang)
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko ta fannin a duniya.
Har wa yau, daga cikin tashoshin jiragen ruwa 10 da suka fi hada-hadar kayayyaki a duniya, akwai tashoshin jiragen ruwan kasar Sin guda 8, ta fannin hada-hadar kwantenoni kuma, guda 6 na kasar Sin ne. (Mai fassara: Bilkisu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp