An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa
Published: 1st, February 2025 GMT
A jiya Jamu’a, wakilin CMG ya samu labari daga ofishi mai kula da aikin ceton mutane daga bala’in girgizar kasa da ya abku a gundumar Tingri karkashin birnin Shigatse na kasar Sin cewa, yanzu haka, an kafa gidajen wucin gadi 7733, da tantuna 9941, tare da tsugunar da mutane 47787 da bala’in girgizar kasa ya ritsa da su.
A ranar 7 ga watan Janairun da ya gabata ne dai, aka samu abkuwar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 6.8 a gudumar Tingri ta birnin Shigatse dake jihar Xizang ta Sin. Kana a halin yanzu, ban da mutanen da aka tsugunar da su cikin gidaje na wucin gadi da tantuna, ganin yadda bala’in girgizar kasa ya lalata gidajensu sosai, akwai wasu mutane 10772 da gidajensu ba su lalace sosai ba, wadanda aka yi bincike kan gidajensu, sa’an nan aka tabbatar da cewa za su iya ci gaba da rayuwa cikin tsoffin gidajensu, kuma babu bukatar tsugunar da su cikin gidajen wucin gadi ko tantuna. (Bello Wang)
কীওয়ার্ড: in girgizar kasa tsugunar da
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas: Matakin Netenyahu Na Dakatar Da Shigar Kayan Agaji Cikin Gaza Keta Yarjejeniya Ne
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji.
Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin da Netanyahu ya dauka na dakatar shigar da kayan agaji cikin Gaza, wata tsokana ce, kuma laifin yaki ne sannan uwa uba keta yarjejeniyar datakar da wuta da musayar fursunoni ce.
Bugu da kari, kungiyar ta Hamas ta ce bukatar da Netanyahu ya gabatar na tsawaita zango na farko na yarjejeniyar, wani yunkuri ne na gujewa aiwatar da ita kanta yarjejeniyar.
Haka nan kuma Hamas ta bukaci Amurka da ta daina zama mai goyon bayan manufofin Netanyahu, tana mai jaddada cewa duk wani kokari na take hakkokin Falasdinawa ba zai haifar da da, mai ido ba.