Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (5)
Published: 1st, February 2025 GMT
Hakanan ma akwai su yi aiki duk irin halin da suka samu kansu, su san yadda lamurran ilimi za su tafi kamar yadda ya dace.Ko mai dai menene hanyoyin ko wuraren da jami’an ilimi za su iya yin aiki suna da yawa da kuma yadda za su samu ci gaba ta kowane hali suka tsinci kansu.Ko dai suna aiki a makarantar lardi ko hukumar da ke karkashin gwamnati,ko hukumar wadda ita babu ruwanta da riba, jami’an ilimi suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da duk wadanda suke son ilimi ana koya masu ta nagartattar hanyar da za ta kasance da hanyoyin karuwa.
Irin ayyukan da jami’in ilimi zai iya yi
Jami’inilimi kwararre ne wanda kuma har ila yau alhakin tafiyar harkokin,manufofin,da tsare- tsaren ilimi suka rataya a wuyansa, wannan ma har ya hada da yadda za a cimma nasarar yin hakan.Suna yin ayyuka a hukumomi daban- daban da suka hada da makarantu, kwalejoji, jami’oi, da kuma hukumomin gwamnati.Babban aikin su shi ne samar da kuma gabatar da tsare- tsare wadanda za su taimakawa ci gaban lamurran ilimi.Hakanan ma suna aiki kafada- kafada da Malamai, ‘yan makaranta, Iyaye, da sauran masu fada aji, domin tabbatar da cewar na tafiyar da lamurran ilimi kamar yadda ya dace, su kuma wadanda ake koyawa suna fahimtar abinda ake koya masu. Hakanan ma ayyukan da za su iya yi jami’an ilimi suna da yawa sun kuma sha bamban.Suna ma iya yin aiki a bangarorin kamar su yadda za a tsara ci gaban koyarwa, horar da Malami,yadda za a rika bibiyar tsarin ilimi, da kuma binciken ilimi.Jami’an ilimi suna iya kasancewa wadanda suka kware a fannoni ko bangarori daban daban kamar karatun/ilimin rayuwar farko ta yaro, bangaren yaki da jahilci, ilimi na musamman, da kuma ilimin koyon sana’oi.
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗaliban Jami’ar Binuwe Da Aka Sace Sun Sami Ƴanci
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp