Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kaddamar Da Wasu Sabbin Makamai Masu Linzami
Published: 1st, February 2025 GMT
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kaddamar da sabbin na’urori masu linzami da na tsaro
Babban sakataren rundunar da ke sa ido kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya sanar da kaddamar da wasu sabbin na’urori masu linzami da na tsaro a cikin tsarin baje kolin “Malik Ashtar”, wanda za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa a kasar.
Birgediya Janar Hamid Bazmashahi ya kara da cewa a wani taron manema labarai a yau Asabar, za su yaye shamakin makaman dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kare karfinsu bisa tsarin baje kolin.
Ya yi nuni da cewa, baje kolin zai hada da, a karon farko, baje kolin jami’an tsaron da ke sintiri da jiragen ruwa masu dauke da aluminium, baya ga nasarorin da aka samu a fannin fasahar kere-kere da Karin adadi makamai.
Ya kara da cewa yana ganin dakarun kare juyin juya halin Musulunci a matsayin wata cibiya da ke da ayyuka da yawa a matakin duniya baki daya, kuma baje kolin zai tattauna wani bangare na ayyukan dakarun kare juyin juya halin da kuma yada shi ga kafafen watsa labarai.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: dakarun kare juyin juya halin Musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Zartarwa Ta Tarayyar Najeriya Ta Amince Da Kirkirar Sabbin Jami’oi 11
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i 11 a cikin kasar.
Ministan ilimi na kasar ta Nijeriya Tunji Alausa ya bayyana cewa; amincewa da kafa sabbin jami’oin da shugaban kasa ya yi, yana nuni ne da yadda ya mayar da hankali wajen ganin ilimi ya isa ga koma.
Wani abu da gwamnatin tarayyar ta amince da shi, shi ne ware kudade da su ka kai dala miliyan 1.67 domin harba tauraron dan’adam da zai rika kula da wuraren hako ma’adanai.