Kasuwar Fina-Finan Sin Ta Dire Matsayi Na Daya A Duniya Na Wucin Gadi A 2025
Published: 1st, February 2025 GMT
Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya.
এছাড়াও পড়ুন:
An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.
A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22 a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.
A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.
Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.
Oluyede ya kara da cewa, rundunar soji ta samar da Uniform guda 100,000 yayin da aka ware naira miliyan dubu domin ciyar da sojojin a kowane wata.
A kwanakin baya ne wata kungiyar da aka fi sani da Mahmuda ta bulla a kananan hukumomin Kaiama da Baruten na jihar Kwara yayin da wasu da ba a tantance ba suka kashe mutane bakwai a Ilesha Baruba da ke karamar hukumar Baruten a jihar Kwara ranar Litinin.
COV/ALI RABIU