Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan.

Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja.

Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa.

Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi abin koyi ne da ya kamata sauran jihohi su bi sahu.

“Mun gudanar da kididdiga a kasa baki daya game da abubuwan da suka shafi kiwo a fadin, wadanda suka hada da wuraren kiwo, hanyoyin shanu, da ruwa da ake da shi ta hanyar madatsun ruwa, da kasuwannin kiwo a fadin kasar nan.

“Muna farin ciki da ci gaban da aka samu a jihar Jigawa.”

“Tsarin samar da zaman lafiya a jihar Jigawa a yau abin koyi ne da zan ba da shawarar sauran jihohi su koya.

“Na san jihar Jigawa ta kasance daya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar manoma da makiyaya.

“Na yaba da yadda jihar take bin tsarin samar da zaman lafiya na gargajiya da muka gada a baya, a yau, babu wani makiyayi da zai shiga kowace karamar hukumar Jigawa ba tare da karbar izini ba.”Inji Ministan.

Tun da farko a jawabinsa,
Gwamna Mallam Umar Namadi, ya bayyana bangarorin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihar Jigawa da suka hada da dabarun karfafa saka hannun jari a harkar kiwon dabbobi, da shata hanyoyin da dabbobi ke bi domin magance rikicin manoma da makiyaya, da sauransu.

Ya kuma jaddada mahimmancin hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnatocin jihohi da ma’aikatar tarayya, domin ganin an samar da hanyoyin da ba za a iya amfana da sana’ar kiwo a Najeriya, inda ya bayyana cewa fannin na da matukar muhimmanci wajen inganta samar da abinci, da ayyukan yi, da bunkasa tattalin arzikin kasa.

“Mun zo nan ne domin tayaka murnar wannanmatsayi da ka samu, kun zo a daidai lokacin da aka mutukar bukatar irin wannan ma’aikatar a kasar nan.

“Wannan ma’aikatar na da matukar muhimmanci, musamman wajen tafiyar da ajandar farfado da ci gaban kasa ta  mai girma shugaban kasa, ta fuskar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan”

Gwamna Namadi ya ce “Mu a jihar Jigawa mun riga mun tsunduma cikin wannan fanni domin noma na cikin ajandarmu guda 12, inda aka bada fifiko  wajen bunkasa kiwon dabbobi”.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Jigawa a jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya

Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a.

Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da ke dauke da makamai su mika makamansu, tare da kauracewa daukar wani mataki kan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
  • Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
  • Gwamnatin Kano Da NBC Sun Shirya Taron Bita Domin Tsaftace Harkar Siyasa
  • Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
  • Shawarar Tabbatar Da Tsaro A Duniya Ta Samar Da “Kyakkyawan Fata” Ga Duniya Mai Fama Da Tashin Hankali
  • Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Kan Aikin Inganta Hadin Gwiwar Jama’a Da Soja
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyayi Da Dabbobi 4 A Wani Hari A Filato
  • Putin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da Iran
  • Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
  • Motar hatsi kashe masu bikin Ista 5 a Gombe