Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Kasarsu
Published: 2nd, February 2025 GMT
Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara.
Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar.
Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ .
Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar yadda gwamnatin shugaba Trump take son ta yi ba.
Dangane da wannan gwamnatin kasar Saudiya ta da gwamnatin kasar Faransa zasu za su dauki nauyin gudanar da taro na musamman kan wannan shawara da shugaban kasar Amurka ya gabatar a cikin watan yuni mai zuwa. Sannan zasu karfafa shawarar samar da kasashe biyu a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, a matsayin hanya tilo ta warwaren wannan matsalar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa.
“Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.”
Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami.
A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya, domin kokarin warware matsalolin da suka jefa kasashen biyu cikin tabarbarewar diflomasiyya.
Bayan ganawa da shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, Jean-Noël Barrot ya bayyana muradin kasashen biyu na “sake gina dangantakar abokantaka.”
A daidai lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka tsakanin Algiers da Paris, ofishin mai gabatar da kara na Faransa ya tuhumi, wasu ‘yan kasar Aljeriya uku, a ranar 11 ga Afrilu, ciki har da wani jami’in ofishin jakadanci, da zarginsu da hannu a sace wani dan adawar gwamnatin Algeria, Amir Boukhors, da aka sani da “AmirDZ na Paris” a cikin 2024.
Aljeriya ta yi kakkausar suka a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, don nuna adawa da kamawa da tsare daya daga cikin jami’an ofishin jakadancinta a kasar Faransa tare da neman a gaggauta sakin shi.