Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu
Published: 2nd, February 2025 GMT
Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa.
Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci.
Marigayi Shehin Malami a Sashen Harshen Larabci na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina, inda a nan ya samu matsayin Farfesa.
Ya kasance Shugaban Sashen Larabci (HOD) na Jami’ar na farko tun da aka kirkiro ta a shekarar 2006, inda ya yi wa’adi biyu na tsawon shekara goma zuwa 2016.
Shi ne mutum na farko ɗan asalin Jihar Katsina da ya samu muƙamin Farfesa a fannin harshen Larabci.
Haka kuma yana daga cikin malaman da suka ƙaddamar da Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Ka Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a Jihar Katsina.
An haife shi a ranar 15 ga Fabrairu, 1953 unguwar Adoro da ke garin Katsina, kuma ya rasu yana da shekara 72, ya bar ’ya’ya 10 da jikoki 32.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Katsina
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa
’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa.
Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa Rubochi.
Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a KanoWani ɗan uwan mamatan, Shuaibu Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun nemi iyalan waɗanda lamarin ya shafa su biya wa kowa Naira 500,000 amma Naira 500,000 suka iya tattaraws baki ɗayansu.
“Shugaban maharan ya kira mu ranar Juma’a, muka sanar da shi cewa Naira 500,000 kacal muka samu. Ba mu san cewa tuni sun kashe su ba saboda jinkirin biyan kuɗin fansar ba,” in ji shi.
Abdullahi ya ce bayan haka, ’yan bindigar sun saki makiyayin da matar da suka sace bayan an biya su Naira miliyan uku a maɓoyarsu da ke cikin dajin Kotonkarfe, a Jihar Kogi.
Shugaban yankin Gwargwada, Ugbada Alhaji Hussaini Agabi Mam, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace matasan ne a hanyarsu ta dawowa daga Rubochi.
“Abin takaici, an kashe matasan nan biyu saboda kawai danginsu sun yi jinkiri wajen biyan kuɗin fansa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ba a samu gawarwakin mamatan ba domin an kai su cikin dajin Kotonkarfe.
“Na samu labarin cewa shugaban Ƙaramar Hukumar Kotonkarfe ya tura maharba da jami’an tsaro don su shiga dajin su nemo gawarwakin, amma har yanzu ba su same su ba,” in ji shi.
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.