Aminiya:
2025-02-22@06:41:14 GMT

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Published: 2nd, February 2025 GMT

A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano ya fitar saboda magance barazanar tsaro da yake fuskanta, ya fara aiwatar da dokar hana motoci masu baƙin gilas wato tinted glass shiga harabar asibitin.

Mahukuntan asibitin sun bayyana cewa, motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su iya shiga, amma sai an bi ka’idojin tsaro na musamman.

Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani

A wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na asibitin, Usman Rabiu Mudi ya fitar, ya ce, an kafa dokar hana motocin masu baƙin gilashi shiga ne saboda wasu munanan abubuwan da suka faru.

Ya bayyana irin munanan ababen kamar yunƙurin sace mutane ta amfani da irin waɗannan motocin da kuma aikata ayyukan laifi daban-daban da suka ƙunshi sata da aikata abubuwan da ba su dace ba a cikin harabar asibitin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ma’aikatan asibitin da ke amfani da mota za su yi rajistar motocinsu a ofishin tsaro don samun tambarin tantancewa da izinin shiga.

A cewar rahotanni, satar motoci da babura da sauran kayayyaki masu daraja ta yi yawa a cikin harabar asibitin.

Haka kuma, an gano cewa, wasu mutane na amfani da harabar asibitin wajen aikata ayyukan ashsha, wanda hakan ya sa mahukuntan suka ɗauki wannan mataki na hana motoci masu baƙin gilashin shiga, don kare rayukan ma’aikata da marasa lafiya da baki.

Wani ɗalibi mai suna Ahmad Bala, wanda ya zo asibitin da mota mai baƙin gilashi, an dakatar da shi daga wurin jami’an tsaron da ke bakin ƙofa.

Ya ce, wannan doka tana da amfani, amma ya buƙaci a cire dalibai daga dokar.

“An dakatar da ni saboda baƙin gilashi, amma ni ɗalibi ne kuma ina goyon bayan wannan mataki.

“Amma ina ganin ya kamata a cire ɗalibai daga wannan doka saboda wannan asibitin koyarwa ne, kuma ɗalibai da dama suna zaune a cikin harabar asibitin,” in ji Bala.

Shugaban tsaro na asibitin, Sani Ahmad Mahmud ya bayyana cewa, matakin hana shigar motoci masu baƙin gilashin yana cikin manufofin kare ma’aikata da marasa lafiya da baƙi da ke zuwa asibitin.

“Wannan mataki ya zama wajibi saboda ƙalubalen tsaro da muke fuskanta. Ina kira ga jama’a su bi wannan doka tare da girmama ta, domin matakin yana cikin muradinsu,” in ji Mahmud.

Wasu daga cikin jama’a sun yaba da matakin, suna ganin hakan zai rage yawaitar shigar miyagun mutane cikin asibitin, inda suke amfani da damar babban harabar wajen aikata laifuka da ayyukan da ba su dace ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: harabar asibitin

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun Kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran itace.

Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano

Har ila yau, ya ce wani ɗan sa-kai na daga cikin waɗanda aka sace.

“A halin yanzu, ’yan bindiga suna cikin dajin Akare. Sun sace ɗaya daga cikin ‘yan sa-kai, kuma yana da bindigogi biyu a tare da shi lokacin da suka yi awon gaba da shi.

“Ba mu san abin da za mu yi a yanzu ba. Mun shafe tsawon ranar ɗaya muna fafatawa da su. An kashe ɗaya daga cikin ’yan sa-kai da kuma wani mai saran itace,” in ji shi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa har kawo hanzu ’yan bindigar suna cikin dajin tare da shanun da suka sace a yankin.

An ruwaito cewa sun kama mai saran itacen, tare da tilasta masa ya nuna musu hanya, sannan suka harbe shi.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaro da ’yan sa-kai na ci gaba da ƙoƙarin bin sahun ‘yan bindigar.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Mun ga ’yan bindigar suna tafiya da babura, uku-uku a kan kowanne.

“Suna wucewa ta wajen da suka saba bi a Kundu, a Ƙaramar Hukumar Rafi, sun nufin Ƙaramar Hukumar Mashegu tare da shanun da suka sace.”

Wani mazaunin Ƙaramar Hukumar Rafi, ya ce ’yan bindigar sun kuma kai hari wasu ƙauyuka a gundumar Gunna da safiyar ranar Laraba, inda suka ƙone rumbunan doya.

Da yake tabbatar da harin, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya), ya ce, an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.

“An riga an tura jami’an tsaro zuwa yankin, kuma suna bin sahun ’yan bindigar.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Wasan Kareti Ta Iran Ta Zama Gwarzo A Asyia
  • Jirgin Saman Da Kasar Sin Ta Kera Mai Amfani Da Lantarki Ya Yi Tashin Farko Cikin Nasara
  • Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro
  • Masu Sana’ar Kamun Kifi Sun Koka Kan Ƙarancin Kuɗaɗen Shiga A Taraba
  • Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu
  • Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
  • ‘Yansanda Sun Kwato Motoci 7 Da Aka Sace Da Taimakon Na’urar e-CMR A Kano
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja
  • Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro
  • Gwamnatin Niger Ta Hana Yan Najeriya Dauke Da Passpor Ta Na ECOWAS Shiga Kasar