Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin.

Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iyaye Mata Sun Bukaci A Rika Samar Da Kayayyakin Bada Tazarar Haihuwa Akan Lokaci

Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da  gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali.

Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa.

Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata.

“Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar kada na samu ciki kafin a kawo wadannan magunguna da ake badawa kyauta.” in ji ta.

Wata mai suna Maryam Abubakar, ta bayyana cewa tana kashe kudi masu yawa wajen zuwa asibiti don dubawa ko kayan sun samu.

Ta koka da cewa siyan kayan bada tazarar haihuwa daga shagunan magani a waje yana da tsada sosai wanda hakan yana hana mata damar siya.

A madadin mata na jihar, ta yi kira ga gwamnati da kungiyoyin agaji da su kawo musu dauki domin mutane da dama suna rungumar tsarin tsara iyali a matsayin mafita ga matsalolin da ke damun al’umma.

A gefe guda, wata ma’aikaciyar lafiya a cibiyar kula da lafiya ta Kachi, Amina Sulaiman, ta tabbatar da cewa kayayyakin samar da tazarar haihuwa sun kare a asibitin tun watanni biyu da suka wuce.

“Muna  takaicin yadda  mata sukan zo don yin tsarin iyali amma babu biyan bukata saboda rashin kayan aiki da magunguna”.

Hajiya Amina Sulaiman ta yi kira ga  hukumomin da abin ya shafa da ssusamar da kayayyakin don ragewa mata radadin rayuwa.

A bara ne gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamiti mai mambobi ashirin da uku kan Lafiyar Uwa, da ke da alhakin farfado da hanyoyin kula da lafiyar uwa a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, yayin kaddamar da kwamitin a ofishinsa, ya bayyana cewa aikin kwamitin ya hada da duba yadda ake aiwatar da shirin Lafiyar Uwa da kirkirar tsarin aiwatarwa domin karfafa abinci mai gina jiki da shawarwari don samun kulawa da uwa da jarirai.

Sauran ayyukan sun hada da yin bincike kan yadda shirin ke gudana da kirkirar hanyoyi don karfafa tura mata zuwa cibiyoyin lafiya daga cikin al’umma.

Yayin kaddamar da kwamitin, Malam Bala Ibrahim ya kara da cewa an fara aiwatar da shirin ne a shekarar 2006 karkashin shirin tallafin  na DFID.

Ya ce daya daga cikin muhimman sassa na shirin shi ne tsarin daukar gaggawa, inda aka samar da motoci don daukar mata masu nakuda zuwa cibiyar lafiya mafi kusa don samun ingantacciyar kulawa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maza da mata da dama daga yankunan karkara a jihar Jigawa sun rungumi tsarin bada tazarar haihuwa da shirin Lafiyar Uwa, suna kuma cin moriyar su ta bangaren lafiya da tattalin arziki.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha  A cikin Kasar
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Iyaye Mata Sun Bukaci A Rika Samar Da Kayayyakin Bada Tazarar Haihuwa Akan Lokaci
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 108
  • MDD Ta Bukaci Taimako Dangane Rikicin Sudan Wanda Ya Isa Kasar Chadi