Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun ce rundunar kai daukin gaggawa mai fada da sojojin kasar Sudan ta kai wa garin “Tandalti” hari da jirgen sama marasa matuki jim kadan bayan ziyarar shugaba majalisar shugabancin kasar Janar Abdulfattah al-Sisi.

Majiyar sojan kasar Sudan ta ce, sun yi amfani da na’urorin kakkabo jiragen sama, akan hare-haren na rundunar kai daukin gaggawa tare da kakkabo da dama daga cikinsu.

Wadannan hare-haren dai sun faru ne jim kadan bayan wata ziyara da shugaban majalisar shugabancin kasar ta Sudan janar Burhan Abdulfattah ya kai garin “Um-Ruwabah’ wanda sojojin Sudan din ba su dade da kwato shi ba.

A cikin makwannin bayan nan dai sojojin na Sudan suna cigaba da samun nasara akan dakarun kai daukin gaggawar tare da kwace garuruwa masu muhimmanci daga wurinsu.

Sojojin na Sudan sun kori mayakan dakarun kai daukin gaggawa daga cikin yankin Aljariza dake kusa da babban birnin kasar ta Khartum.

A gefe daya wata kungiya ta likitocin kasar ta Sudan ta sanar da cewa mutane 61 su ka rasa rayukansu sanadiyyar harin da rundunar kai daukin gaggawa ta kai wa kasuwar birnin Umdruman, yayin da wasu mutanen masu yawa su ka jikkata wasu  da dama.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kai daukin gaggawa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin

Hukumar birnin istambul ta bada sanarwan dakatar da Akram Imamoglu daga matsayinsa na magajin garin birnin Istambul na wucin gadi, har zuwa lokacinda za’a tabbatar da kubutarsa daga abubuwan da aka zarginsa da su.

Tashar talabijin ta Almayaddeen ta kasar Labanon ta nakalto mahukunta a birnin Istambul na bada labarin cewa za’a zabi wanda zai maye gurbinsa na wucin gadi a ranar Laraba mai zuwa.

Labarin ya kara da cewa ana zirgin Imamoglu da karban rashawa da cin hanci da kuma kafa kungiyar yan ta’adda.

Kama Imamoglu magajin garin na birnin Istambul dai a makon da ya gabata, ya sa dubban daruruwan masu goyon bayansa a birnin  Istambul da wasu birane a kasar suka fito kan tituna tare da bukatar a sake shi.

Ana ganin Imamoglu zai iya zaman dan takarar shugaban kasa wanda zai iya kada shugaba Ordugan a zaben shugaban kasa mai zuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin
  • Amurka ta sake kai hare-hare Yemen
  • Sudan: Sojoji na ci gaba karbe mahimman gine-gine a birnin Khartoum
  • Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
  • Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Fadar Shugaban Kasa A Birnin Khartum
  •  HKI: Ana Samun Koma Bayan Sojojin Sa-Kai Da Suke
  • Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Yaffa Kusa Da Tel Aviv A Karo Na Biyu A Cikin Sa’o’i 24
  • Gwamnatin Yobe na ciyar da almajirai a Tsangayu 85 kullum