A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin.

Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda ba zai ba da damar daidaita matsalar da kasar Amurka ke fuskanta ba, maimakon haka, zai lalata huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

Ban da haka, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta ce, kasar Sin za ta kai kara ga kungiyar cinikayya ta duniya, da daukar matakai don mayar da martani ga matakin Amurka.

A sa’i daya kuma, kasar Amurka ta ce za ta sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 25%, kan kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Mexico da Canada. Ban da haka, shugaban kasar Donald Trump ya ce yana duba yiwuwar kakaba karin haraji kan kayayyakin da ake shigar da su kasar Amurka daga kasashen Turai, ganin yadda kungiyar kasashen Turai EU ta hana shigowar motoci da amfanin gona na kasar Amurka cikin kasuwannin kasashen Turai, a lokacin da ya yi hira da ‘yan jaridu a kwanan baya. (Bello Wang)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Amurka

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masanin Amurka: Matakan Kariyar Cinikayya Da Amurka Ke Aiwatarwa Babban Kuskure Ne
  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
  • Jakadan Sin A Amurka: Mayar Da Karin Haraji Makami Kaikayi Ne Da Zai Koma Kan Mashekiya
  • Iran Ce Kasar Wacce Ta Fi Shigar Da Kayakin Kasuwanci Zuwa Kasar Afganistan A Shekarar Da Ta Gabata
  • Amurka ta cire tukuicin wanda ya bayar da bayani kan mataimakin shugaban Taliban
  • Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  
  • Wike Ya Kwace Filaye 4,794 A Abuja Saboda Rashin Biyan Kudin Ka’ida
  • Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa
  • Iran, ta yi Tir da kwamatin tsaro kan rashin tabaka komai na takawa Amurka da Isra’ila birki