Hamas Ta Yi Tir Da Shawarar Shugaban Amurka Ta Kwashe Falasdinawa Daga Gaza
Published: 2nd, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita.
A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya yi tir da irin wadannan shawarwari a matsayin “abin dariya kuma maras amfani,” yana mai cewa, “Abin da mamayar Isra’ila ta kasa cimma da karfi, ba zai samu ta hanyar makircin siyasa ba.
Abu Zuhri ya kara da cewa, “Sanarwar da Amurka ta nanata na raba Falasdinawa da gidajensu da nufin sake gina yankin zirin Gaza na nuni da yadda kasar ke da hannu wajen aikata laifukan da suka shafi yanki.”
Kana, ya yi gargadin cewa, “aikin kwashe mazauna Gaza” wani makirci ne na kara hargitsi da tashin hankali a yankin.
A ranar 25 ga watan Janairu ne dai Trump ya gabatar da wannan tsari mai cike da cece-kuce na kwashe Falasdinawa daga Gaza zuwa Masar da Jordan, wanda kasashen biyu suka ki amincewa da shi matuka.
Shi dai Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada kiransa ga kasashen Masar da Jordan domin su karbi Falasdinawan Gaza da suka rasa matsugunansu, duk da cewa kasashen Larabawan biyu sun yi watsi da shawararsa da ke cike da ce-ce-ku-ce.
Haka su ma kasashen Qatar, UAE da kuma Saudiyya sun yi fatali da shawarar da Trump ya bayar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berry ya bayyana cewa HKI tanason jawosu cikin tattaunawar diblomasiyya wanda zai kai kasar ga samar da huldar jakadanci da ita, amma mu bama tare da wannan ra’ayin.
Nabih Berry ya bayyana haka ne a lokacinda yake zantawa da jaridar ‘Sharqul Awsad’ ya kuma kara da cewa a halin yanzu muja jiran HKI ta aiwatar da dukkan abubuwan da suka zo cikin yarjeniyar tsagaita wuta ta 1701 wacce kasashen duniya suka amince da ita, amma HKI ta ki aiwatar da ita a yayinda kungiyar Hizbullah ta luzumci tsagaita budewa juna wata na wannan yarjeniyar.
Shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya kara da cewa, a halin yanzu HKI take ficewa daga kasar Lebanon daga wasu wurare kimani biyar wanda hakan ya hana sojojin kasar Lebanon shiga wurare don tabbatar da cewa suna kula da dukkan kan iyakoki na kasar. Banda haka sojojin HKI suna keta hirumin wannan yarjeniyar, wanda yakata a aiwatar da ita watanni 6 da suka gabata. Tana kai hare-hare a kudancin kasar da kuma wasu wurare a Biqaa.